Sport
Dollar
40,9411
0.09 %Euro
47,9607
0.44 %Gram Gold
4.383,8900
0.13 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hukumar ta ce za a buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta ta hanyar tasharta, cvr.inecnigeria.org.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya ta ce za a fara gudanar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a na shekarar 2025 a duk faɗin ƙasar a ranar 18 ga watan Agusta.
INEC ta bayyana hakan ne a shafinta na X ranar Juma'a.
Hukumar ta ce za a buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta ta hanyar tasharta, cvr.inecnigeria.org.
Ya bayyana cewa za a fara rajistar mutanen nan da mako guda, ranar 25 ga watan Agusta.
A cewarta, za a gudanar da wannan aiki a duk fadin kasar a dukkan ofisoshin kananan hukumomin da kuma wuraren da aka keɓe.
INEC ta ce za a gudanar da aikin ne daga ranar Litinin zuwa Juma'a, daga karfe 9 na safe zuwa karfe 3 na rana.
"Kuri'unku sun ta’allaƙa ne da yin rajistarku. Ka da ku rasa damarku ta yin rajista," in ji shi.
A bisa ƙa’ida ‘yan shekara 18 zuwa sama ne kawai ke da izinin yin zaɓe a Nijeriya.
A shekarar 2027 ne za a sake yin manyan zaɓuka a Nijeriya.
Comments
No comments Yet
Comment