Dollar

42,8229

0.04 %

Euro

50,3593

0.38 %

Gram Gold

6.106,3000

2.24 %

Quarter Gold

9.975,1400

1.12 %

Silver

94,3300

1.96 %

Shugaba Kagame ya ce coci-coci da yawa "na satar kuɗi ne kawai," kuma wasun su sun zama “matattarar ɓata-gari.”

Hukumomi sun rufe dubban coci-coci a Rwanda kan karya doka

Hukumomi a Rwanda sun rufe majami'u fiye da 10,000 na cocin Kirisocin Bishara (Evangelical) saboda rashin bin dokar da aka tsara ta 2018 don tafiyar da harkokin wuraren ibada.

Dokar ta gabatar da sabbin ƙa’idojin kula da lafiya, tsaro, da kuma bayyana bayanai kan harkokin kuɗi kuma tana buƙatar duk masu wa'azi su samu horo.

Shugaba Paul Kagame ya yi ta suka a kan cocin ‘yan bishara ta Evangelical da suka yaɗu sosai a faɗin ƙaramar ƙasar da ke yankin Manyan Tafkunan Afirka.

"Idan ta ni ne, da ba zan ma sake buɗe coci ko ɗaya ba," Kagame ya faɗa wa manema labarai a watan da ya gabata.

"A duk ƙalubalen ci-gaba da muke fuskanta, yaƙe-yaƙe, kuɓutar ƙasarmu, mece ce rawar da waɗannan coci-coci ke takawa? Shin suna kuma samar da ayyukan yi? Da yawa suna sata ne kawai; wasu majami'u kawai suna ɓoye 'yandaba ne," in ji shi.

Mafi yawan 'yan ƙasar Rwanda Kiristoci ne, a cewar ƙidayar jama'a ta 2024, inda da yawa yanzu suna tafiya mai nisa da tsada don neman wuraren yin ibada.

Dokar 2018 ta buƙaci majami'u su gabatar da shirye-shiryen aiki na shekara-shekara waɗanda ke bayyana yadda suka dace da "ƙa'idojin ƙasa" da gwamnati ta tanada.

Dole ne a bayar da dukkan gudunmawa ga coci ta hanyar asusun da aka yi rajista a banki.

‘Al’ada tun zamanin mulkin mallaka’

Malamin kiristoci Sam Rugira, wanda aka rufe rassan cocinsa guda biyu a bara saboda rashin cika ka'idojin kare gobara, ya ce dokokin sun fi shafar sabbin majami'un bishara da suka "yaɗu sosai" a 'yan shekarun nan.

Amma Kagame ya bayyana coci-cocin a matsayin wasu kayan tarihi na lokacin mulkin mallaka da har yanzu ƙasar ke fama da shi.

"‘Yan mulkin mallaka sun yaudare ku, kuma kun bari an yaudare ku," ya faɗi haka a watan Nuwamba.

Amma wasu sun ce matakin da aka ɗauka kan wuraren ibada na da alaƙa da kisan ƙare-dangi na 1994 kan 'yan Tutsi, inda aka kashe kimanin mutane 800,000.

Ismael Buchanan, malamin kimiyyar siyasa a Jami'ar Ƙasa ta Rwanda, ya ce wani lokacin coci-cocin na iya zama "hanyar ɗaukar mayaƙa" ga Mayaƙan Dimokuraɗiyya don 'Yantar da Rwanda (FDLR), 'yan tawayen Hutu da aka kafa bayan gudun hijira a Jamhuriyar Kongo.

"Na yarda cewa addini da imani sun taka muhimmiyar rawa wajen warkar da mutanen Rwanda daga raunukan da suka shafi ƙwaƙwalwa da tunani bayan kisan ƙare-dangi, amma kuma ba shi da ma'ana a samu coci a nisan kowane kilomita biyu maimakon asibitoci da makarantu," in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#