Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta jaddada goyon baya na samun haɗin kai da 'yancin ƙasa na Sudan sannan ta gargaɗi dakarun RSF cewa za su fuskanci hukunci kan laifukan da suke aikatawa a kan fararen-hula.
Wakilin Ƙungiyar Tarayyar Afirka a Sudan, Mohamed Belaiche, ranar Jumma’a ya ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) za su fuskanci hukunci kan hare-haren da suka “kitsa” kuma suke kai wa fararen-hula a ƙasar.
Belaiche ya miƙa wannan saƙo ne ga shugaban Gwamnatin Mulkin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, daga shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Mahmoud Ali Youssouf yayin da suka gana a Port Sudan.
“Muna Allah wadai da kakkausar murya kan hare-haren da RSF take kai wa fararen-hula da kashe mutanen da ba su da laifi da lalata abubuwan more rayuwa,” in ji shi kamar yadda kamfanin dillancin labaran SUNA ya ruwaito.
“Waɗanda suke kitsa wannan ta’asa za su fuskanci hukunci.”
Wakilin na Tarayyar Afira ya ce ganawar da ya yi da Burhan “wata muhimmiyar dama ce ta tattaunawa domin samo hanyoyi mafiya amfani game da ƙokarin da ƙasashen yankin da ma na duniya suke yi wajen samar da zaman lafiya da tsaro a Sudan,” yana mai bayyana ƙasar a matsayin wadda ke da matuƙar muhimmanci ga yankin da kuma ci-gaban ƙungiyarsu.
Belaiche ya ce ya saurari jawabai daga shugabannin Sudan game da halin da ake ciki da kuma yadda za a samu mafita.
Ya jaddada matsayin Ƙungiyar Tarayyar Afirka wajen goyon bayan haɗin kai da ‘yancin Sudan.
“Babu wani gurbi na samar da wata gwamnati ta daban a ƙasar Sudanl,” a cewarsa, inda ya jaddada muhimmancin samar da mafita ta hanyar sulhu da tattaunawa a Sudan.
Kazalika Belaiche ya gana da Firaministan Sudan Kamal Idris, a cewar kamfanin dillancin labarai na SUNA.
Idris ya ce gwamnatin Sudan tana maraba da duk wani yunƙuri ne tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.
Comments
No comments Yet
Comment