Sport
Dollar
42,8203
0.03 %Euro
50,3723
0.4 %Gram Gold
6.106,6400
2.25 %Quarter Gold
9.975,1400
1.12 %Silver
94,4100
2.05 %Ana kallon soke dokar, wadda ta fara aiki daga ranar 10 ga Disambar 2025, a matsayin babbar nasara ga masu fafutukar kare muhalli da ƙungiyoyin farar-hula, waɗanda tun da dadewa suke sukar dokar saboda yadda ta cire wa gandun daji rigar kariya.
Gwamnatin ƙasar Ghana a hukumance ta soke dokar da ta yi wadda ta bayar da damar haƙar ma’adinai a cikin dazukan da aka killace, a wani yunƙuri na kawar da ɗabi’ar nan ta haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba wata “galamsey”.
Ana kallon soke dokar, wadda ta fara aiki daga ranar 10 ga Disambar, 2025, a matsayin babbar nasara ga masu fafutukar kare muhalli da ƙungiyoyin farar-hula, waɗanda tun da dadewa suke sukar dokar saboda yadda ta cire wa gandun daji rigar kariya.
Dokar mai mai lamba ta L.I. 2462 ta ba da damar hakar ma’adinai a cikin gandun dajin da aka killace, lamarin da ya haifar da damuwa kan lalacewar muhalli. Soke dokar na da nufin ƙarfafawa da kuma kiyaye gandun daji da kuma yaki da hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Ministan Filaye da Albarkatun Ƙasa, Mista Emmanuel Armah-Kofi Buah, ne ya gabatar da takardar soke dokar a gaban Majalisa, inda ya jaddada buƙatar kare gandun dajin Ghana da kuma dakile galamsey.
Ƙungiyar kare muhalli ta A Rocha Ghana ta yi maraba da matakin, tana mai jaddada buƙatar ɗaukar matakai cikin gaggawa domin dakatar da ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma farfaɗo da gandun dajin da aka lalata.
Wata sanarwa da ƙungiyoyin farar-hula masu kare muhalli guda 17 a Ghana suka fitar a ranar Alhamis ta bayyana godiyarsu ga gwamnati da Majalisa bisa nasarar soke dokar da ta bai wa hakar ma’adinai damar barazana ga gandun dajin
Ƙungiyoyin sun yaba wa Ministan Filaye da Albarkatun Ƙasa kan ƙoƙarinsa wajen soke dokar.
Ana kallon soke dokar a matsayin wani muhimmin mataki na dawo da gandun dajin Ghana, wanda hakar ma’adinai ya yi wa matuƙar illa.
Comments
No comments Yet
Comment