Sport
Dollar
41,1466
0.24 %Euro
48,1414
0.06 %Gram Gold
4.563,5600
1.2 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Aƙalla 'yan jarida da ma'aikatan kafafen watsa labarai 244 aka kashe a Gaza, tun lokacin da yaƙin Isra'ila ya fara ranar 7 ga watan Oktoba, na shekarar 2023.
Harin sama na Isra’ila kan cibiyar lafiya ta Nasser Medical Complex a Khan Younis ya kashe ‘yan jarida biyar ranar Litinin.
Daga cikinsu akwai mai ɗaukar hoto Moaz Abu Taha da Mariam Abu Daqqa da mai ɗaukar bidiyon gidan talabijin na Palestine TV Hussam al-Masri, da kuma ɗan jaridar Al Jazeera Mohammad Salama da ma’aikacin kwantaragi na Reuters Hatem Khaled, in ji majiyoyin lafiya da kuma kafar watsa labaran da ke Qatar.
Kashe-kashe na baya bayan nan sun nuna irin gagarumar ta’adin da yaƙin ya yi a kan ‘yan jaridan Gaza, lamarin da ya mayar da yankin wuri mafi hatsari ga ‘yan jarida a duniya.
Daga farko a cikin ƙarshen mako, ƙungiyar ‘yan jarida ta Falasɗinu ta tabbatar da cewa harsasan Isra’ila sun harbe Khaled al-Madhoun, wani maiɗaukar bidiyo wa kafar Palestine TV, a yankin Zikim da ke yankin arewacin Gaza yayin da yake ɗaukar bidiyon fararen hula da ke neman taimakon jinƙai.
Kashe kashen sun biyo bayan wani hari na ranar 10 ga watan Agusta a birnin Gaza inda aka kashe ‘yan jaridan Al Jazeera shida.
Comments
No comments Yet
Comment