Dollar

39,1187

-0.08 %

Euro

44,8261

0.55 %

Gram Gold

4.226,3500

0.11 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban na Turkiyya ya ce hanyar bututun Igdir-Nakhchivan shi ne misali na baya bayan nan na haɗin gwiwar makamashi da aka dade da kuma nasarar samu a tsakanin kasashen biyu.

Haɗin gwiwar Turkiyya da Azabaijan kan makamashi na ƙarfafa tsaron yankin: Shugaba Erdogan

Haɗin gwiwar makamashi tsakanin Turkiyya da Azabaijan, ba wai don kawai ya amfanar da kasashen biyu ba ne, har ma da karfafa tsaron makamashi a duk faɗin yankin da nahiyar Turai, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wani sako da ya aika a taron makon makamashi na Baku.

Ci gaban da aka samu a fagen siyasar duniya na baya-bayan nan ya dada jaddada muhimmancin hadin gwiwar Turkiyya da Azabaijan kan tsaron makamashi, kamar yadda Erdogan ya bayyana a cikin sakon wanda ministan makamashi da albarkatun kasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar ya karanto a ranar Litinin a yayin taron wanda ke gudana a Baku babban birnin kasar Azarbaijan.

Haɗin gwiwar, wanda aka alakanta da mahimman ayyukan samar da ababen more rayuwa irin su bututun Baku-Tbilisi-Ceyhan da na Kudancin Caucasus (wanda aka fi sani da bututun Baku-Tbilisi-Erzurum) da kuma bututun iskar gas na Trans-Anatolian (TANAP), ba wai kawai don amfanin Turkiyya da Azerbaijan ba ne, yana dada inganta tsaron makamashi a yankin da Turai, "in ji Erdogan.

Shugaban na Turkiyya ya ce bututun na Igdir-Nakhchivan da aka kaddamar a watan Maris, shi ne misali na baya-bayan nan na haɗin gwiwar makamashi da aka dade da kuma nasarar samu a tsakanin kasashen biyu.

"Soma aikin hanyar bututun man ya karfafa samar da makamashi a yankin Nakhchivan sannan ya kara karfafa mana dangantaka," in ji shi.

Dabarun ayyuka

Kazalika Erdogan ya bayyana cewa, kara samar da wutar lantarki tsakanin Turkiyya da Azabaijan wani aiki ne mai matukar muhimmanci.

Ya kuma bayyana bukatar kara karfin alaka tsakanin Turkiye da Nakhchivan da kuma Turkiye da Jojiya, in ji Erdogan.

"Mun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa kan wutar lantarki da cinikayya don kafa sabuwar hanyar hada wutar lantarki tsakanin Turkiyya, da Azerbaijan, da Jojiya, da kuma Bulgaria."

"Muna da burin kammala wannan aiki, wani mataki mai cike da tarihi na samar da tsaro da wadata a yankinmu cikin gaggawa," in ji shugaban.

Erdogan ya ce, akwai gagarumin damar yin sabbin ayyukan iskar gas tsakanin kasashen biyu.

"Azabaijan, wacce ta dade tana samar da iskar gas mai yawa ga Turkiyya da Turai, tana taka muhimmiyar rawa a kasuwar makamashi ta duniya, rawar da ke da muhimmanci musamman a yanayin da ake ciki," a cewar Erdogan.

"Anan gaba, muna da wata muhimmiyar dama ta karfafa haɗin gwiwarmu kan fitar da iskar gas ta Turkmen zuwa kasashen Azabaijan da Turkiyya ta yadda za ta amfanar da dukkan bangarorin," in ji Erdogan, yana mai cewa "Wannan aikin zai taimaka wajen rarraba hanyoyin samar da kayayyaki da kuma ba da gudummawa ga ci gaban yanki."

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#