Sport
Dollar
38,8949
0.36 %Euro
43,4533
-0.25 %Gram Gold
3.997,1000
-0.9 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Abba El-Mustapha ya ce sun samu ƙorafi daga jama’ar gari da malamai da ‘yan kasuwa wanda hakan ya sa aka haramta wannan biki.
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta haramta bikin ƙauyawa day da kuma soke lasisin duk wani gidan gudanar da bukukuwa ko kuma event center a jihar.
Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai a ranar Asabar.
Wannan na zuwa ne a yayin da mutane da dama ke ƙorafi a shafukan sada zumunta game da shiga ta rashin kamala da wasu mata ke yi a lokacin bikin.
Shugaban hukumar ya ce sun samu ƙorafi daga jama’ar gari da malamai da ‘yan kasuwa wanda hakan ya sa aka haramta wannan biki.
Ya kuma ce tuni suka yi haɗin gwiwa da jami’an tsaro waɗanda suka haɗa da ‘yan sanda da hisbah da sauran jami’a domin aiwatar da wannan doka.
Haka kuma Abba El-Mustapha ya bayyana cewa sakamakon gyaran dokar hukumar tace fina-finai da majalisar dokokin ta Kano ta yi wadda gwamnan jihar ya saka wa hannu, sun soke lasisin duk wata event center a jihar inda ya ce ya zama tilas duka irin waɗannan gidaje a Kano su je su sabunta rajistarsu.
Haka kuma ya bayyana cewa sabuwar dokar ta haramta ɗora fina-finai a soshiyal media har sai hukumar ta tace su.
Shugaban hukumar kuma ya gargaɗi masu ɗora abubuwa a kafafen sada zumunta inda ya ce dokar ta ba su damar sa ido kan abubuwan da jama’a ke ɗorawa musamman na nishaɗi.
Ya kuma ce a yanzu dokar ta ba su dama su sa ido kan masu gidajen hoto da gidajen buga takardu da masu zane da masu aikin MC a gidajen biki da kuma masu wasanni a kan titi.
Comments
No comments Yet
Comment