Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Eritrea ta yi kira ga Kwamitin Tsaro na MDD ya yi kakkausan martani kan amincewar da Isra'ila ta yi wa Somaliland, tana gargaɗin cewa matakin zai iya tsunduma yankin da duniya cinkin rashin kwanciyar hankali.
Eritrea ta yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi bayyanannen martani game da amincewar Isra'ila ga Somaliland, tana gargadin cewa wannan matakin na iya haifar da rashin zaman lafiya a yankin da kuma a duniya baki ɗaya.
Ma'aikatar Watsa Labarai ta ƙasar ta fada a wata sanarwa a ranar Lahadi cewa ba yanzu aka fara bin matakin ba, an riga an fara shirya shi tun wani lokaci, kuma yana iya sanadiyyar haifar da "matsaloli masu haɗari da hargitsi ga yankin da ma duniya baki daya.
"Saboda haka, tana buƙatar amsa bayyananniya a matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da mambobinta," in ji sanarwar.
A ranar Jumma'a ne Isra'ila ta bayyana amincewarta da Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Matakin ya jawo suka daga Somaliya, da wasu ƙasashe da kuma Ƙungiyar Tarayyar Afirka.
Ana sa ran Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya za ta tattauna kan al'amarin a ranar Litinin.
Yankin Somaliland ya ɓalle daga Somaliya a 1991, matakin da Mogadishu ba ta amince da shi ba kuma ba, haka al'ummar ƙasa da ƙasa.
Eritrea da Somaliya sun maido da dangantakar diflomasiyya a 2018 bayan shekaru ana tashin hankali, kuma tun daga lokacin sun ƙara haɗin gwiwa a fannin tsaro da haɗin kai na yanki.
Ana sa ran Kwamitin Tsaro zai tattauna game da amincewr ta Isra'ila ga Somaliland a wani zaman gaggawa ranar Litinin.
Comments
No comments Yet
Comment