Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, ba ta faɗi ƙasar da Shugaba Tinubu zai je a Turai ba, da ma kwanakin da zai kwashe a can.

Shugaba Tinubu ya tafi Turai don ci gaba da hutun ƙarshen shekara

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ranar Lahadi ya tashi daga birnin Lagos zuwa ƙasashen Turai domin ya ci gaba da hutunsa na shekara, a cewar fadar shugaban ƙasa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, ba ta faɗi ƙasar da Shugaba Tinubu zai je a Turai ba, da ma kwanakin da zai kwashe a can.

Sai dai ta ce shugaban zai kai ziyara Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bisa gayyatar shugaban Daular.

“Mai Martaba Sheikh Mohamed bin Zayed AlNahyan, shugaban ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya gayyaci Shugaba Tinubu domin ya halarci taro na mako ɗaya kan Ɗorewar Ci-gaba na 2026 (ADSW 2026), wanda za a gudanar a farkon Janairun sabuwar shekara,” in ji sanarwar.

Bayo Onanuga ya ƙara da cewa an saba gudanar da taron domin haɗa shugabannin gwamnati da ‘yan kasuwa da kuma al'umma domin su tattauna kan ci-gaba mai ɗorewa.

Ya ce Shugaba zai koma Nijeriya bayan kammala taron.

A watan Satumban da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya ɗauki kwana 10 domin yin wani ɓangare na hutunsa na shekara inda ya tafi Faransa da Birtaniya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#