Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An kwashe makonni ana taƙaddamar diflomasiyya tsakanin ƙungiyar AES da Nijeriya bayan saukar gaggawa da jirgin saman kirar C-130 ya yi a Burkina Faso sakamakon matsalar na’ura.

Jirgin Saman Sojin Nijeriya C-130 da aka tsare a Burkina Faso ya isa Portugal domin yin gyara

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce jirginta kirar C-130 da ya sauka a Burkina Faso kwanakin baya sakamakon matsalar na’ura, yanzu ya isa Portugal domin a gyara shi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Jumma’a da maraice ta ce jirgin ya “isa wurin gyara na OGMA da ke birnin Lisbon, Portugal ranar Jumma’a cikin aminci”.

Ya ƙara da cewa matuƙa jirgin da sauran sojojin da ke cikinsa suna cikin ƙoshin lafiya.

Jirgin ya tashi ne daga birnin Banjul na ƙasar Gambia inda ya isa Portugal bayan ya samu taimakon wani jirgin ɗaukar kaya domin isa wurin gyara.

A farkon watana Disamba ne jirgin saman dakon kaya na sojin saman Nijeriya ɗauke da sojoji 11 ya yi saukar gaggawa a birnin Bobo Dioulasso na Burkina Faso sakamakon matsalar na’ura.

Sai dai nan-take gwamnatin Burkina Faso ta tsare shi tare da sojojin da ke cikinsa. Daga bisani ƙungiyar AES ta ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar ta yi zargin cewa ta tilasta masa sauka ne saboda ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba.

Wannan lamari ya haddasa tirka-tirkar diflomasiyya har sai da Shugaba Bola Tinubu ya aika ministan harkokin wajen Nijeriya Yusuf Tuggar Burkina Faso wurin shugaban ƙasar Kyaftin Ibrahim Traore domin ba shi haƙuri.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Tuggar, Alkasim Abdulkadir, ya fitar ranar Larabar da ta wuce ta ce ɓangarorin biyu sun warware batun cikin lumana, inda daga bisani aka saki jirgin da sojojin na Nijeriya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#