Sport
Dollar
42,9259
0.13 %Euro
50,6303
-0.18 %Gram Gold
6.252,4200
1.32 %Quarter Gold
10.319,2000
1 %Silver
108,1200
9.12 %Domin martani ga matakin Amurka na dakatar da bayar da bizar shiga ƙasar ga ‘yan ƙasar Nijar, mahukunta a Yamai sun dakatar da bayar da duk wata biza ga ‘yan ƙasar Amurka, in ji majiyoyin diflomasiyya.
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun ɗauki matakin mayar da martani ga takwarorinsu na Amurka inda suka dakatar da bayar da biza ga duk wani Ba’amurke da ke son zuwa Nijar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijar ANP ya rawaito majiyoyin diflomasiyya na ƙasar.
“An ɗauki matakin ne don bayyana ƙarfin iko da ‘yancin Nijar, kuma diflomasiyyarta ba za ta dinga miƙa kai bori yana hau ga kowace ƙasa ba.”
“Nijar ta dakatar da bayar da biza dindindin ga dukkan ‘yan ƙasar Amurka kuma ta hana dukkan Amurkawa shiga ƙasarta sai abin da hali ya yi,” in ji majiyoyin.”
A ranar Talata 16 ga Disamba ne Amurka ta faɗaɗa ƙarin ƙasashen da ta haramta wa jama’arta shiga Amurka da suka haɗa da ƙasashen ƙawancen Sahel na Mali, Nijar da Burkina Faso.
A matakin na Amurka an bayyana ɗaukar matakan “dakatarwa na dindindin” ga masu neman bizar gudun hijira ko gajeren zama a ƙasar.
Gwamnatin Trump ta bayyana “rashin isassun bayanan tantancewa” a matsayin dalilan da suka sanya ta ɗaukar wannan mataki, ba tare da bayyana me ya sa hakan ya shafi ƙasashen AES ba.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta tababa kan bayar da bizar Amurka a ƙasashen Afirka.
A watan Oktoba, Washington ta saka kuɗi daga $5,000 zuwa $15,000 ga ‘yan wasu ƙasashen Afirka da ke son bizar zuwa Amurka saboda yadda suke karya ƙa’idar kwanakin zaman da ake ba su.
Ba da jimawa ba Mali ta ɗauki matakin ramuwa, amma daga baya an cire ta daga jerin ƙasashen ko da yake har yanzu matakin na aiki a kan ƙasashen da suka haɗa da Mauritania, Tanzania, Gambia da Malawi.
A ɓangaren Yamai, wannan martani na bayyana aniyar aika bayyanannen saƙo. Sai dai kuma hakan na iya dagula haɗin kai da musayar ‘yan’adam, tattalin arziki da ilimi a tsakanin ƙasashen.
Ana ci gaba da sanya idanu don ganin ko wannan rikici na diflomasiyya zai ɗauki lokaci mai tsayi ko akasin haka.
Comments
No comments Yet
Comment