Sport
Dollar
42,9259
0.13 %Euro
50,6303
-0.18 %Gram Gold
6.252,4200
1.32 %Quarter Gold
10.319,2000
1 %Silver
108,1200
9.12 %Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Zambia (ACC) ta karrama wata 'yarsanda da ta ƙi karɓar cin hancin dala 50,000 daga wani da ake zargi da yin fasa-kwauri da tsabar kuɗi mai yawa a babban filin jirgin saman Lusaka, babban birnin ƙasar.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Zambia (ACC) ta karrama wata 'yarsanda da ta ƙi karɓar cin hancin dala 50,000 daga wani da ake zargi da yin fasa-kwauri da tsabar kuɗi mai yawa a babban filin jirgin saman Lusaka, babban birnin ƙasar.
Detective Sergeant Ruth Nyambe, wadda ke aiki a filin jiragen sama, ta ƙi karɓar kuɗin da mutumin ya ba ta, wanda a yayin bincike aka yi zargin kama shi da dala miliyan 2.3 lakadan da kuma sandunan zinari guda bakwai a filin jirgin sama na Kenneth Kaunda.
Ƙungiyar 'yansandan Zambia ta ce lamarin ya faru a ranar 5 ga Fabrairun 2025.
ACC ta ce mutumin, wanda ba a ambaci sunansa ba ya fara miƙa wa Nyambe cin hanci na dala 5,000, amma da ta ƙi, sai ya ƙara tayin zuwa dala 50,000 don a bar shi ya ci gaba da tafiyarsa.
'Gaskiya ta musamman'
Kara, Nyambe ta tsaya kan matsayinta, maimakon ta karɓi cin hancin, sai ta kai lamarin ga Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Zambia (DEC), abin da ya kai ga kamun wanda ake zargin.
Jaridar Lusaka Times ta Zambia ta ruwaito cewa wanda ake zargin yana hanyarsa ta zuwa wani wuri da ba a ambata ba daga Lusaka.
ACC ta girmama Nyambe a ranar Talata, 23 ga Disamba, yayin taron manyan jami'an gudanarwa na hukumar yaki da cin hanci a Lusaka.
ACC ta ce ta yi murnar samun jami'a mai 'gaskiya ta musamman a cikin aikin da take yi'.
Ƙarin matsayi
Daraktar Janar ta ACC, Daphne Chabu, ta girmama Nyambe da Kyautar Gaskiya ta hukumar. Ba a bayyana nan da nan ko an ba ta kyautar kuɗi tare da wannan girmamawa ba.
A ranar Laraba, Babban Sufeton 'Yan Sanda na Zambia Graphel Musamba ya ɗaga mukamin Nyambe daga Sergeant zuwa Inspector na 'Yan Sanda.
Sashen 'yan sandan ya ce an ƙara wa Nyambe matsayi ne 'saboda yabawa da gaskiyarta a aikinta, da ƙin karɓar cin hanci'.
A wani ɓangare daban, Sufeto-Janar Musamba ya ɗaga mukamin Sergeant Samuel Mbewe zuwa Inspector bayan ya ƙi karɓar cin hanci na kwacha 20,000 (kimanin $890) daga wani baƙo.
Ƙarin girmamawa da aka yi
Wannan baƙon ya miƙa cin hancin ne bayan ya karya ƙa'idodin zirga-zirga a gundumar Kitwe a lardin Copperbelt na ƙasar a ranar 5 ga Fabrairu, 2025.
Sashen 'yan sandan ya bayyana a ranar Laraba cewa Mbewe, maimakon karɓar cin hancin, ya kama baƙon wanda ke tuƙa motar da ba a yi wa rijista ba.
A halin da ake ciki, hukumar yaki da cin hanci, ACC, a ranar Talata ta kuma yaba wa wani jami'i na ma'aikatar noma ta Zambia saboda ƙin karɓar cin hanci na kwacha 160,000 (kimanin $7,100) daga wani kamfanin niƙa hatsi.
Comments
No comments Yet
Comment