Shugaban Türkiye Recep Tayyip Erdoğan ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da ƙarfafa dangantaka da ƙasashen Afrika bisa daidaito, mutunta juna da moriyar bangarorin biyu.
ANKARA — Shugaban Türkiye Recep Tayyip Erdoğan da Shugaban Nijar Abdourahamane Tchiani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa bayan tattaunawarsu a Ankara.
Erdoğan ya bayyana cewa Türkiye za ta ci gaba da bunƙasa dangantakarta da ƙasashen Afrika bisa ginshiƙan haɗin gwiwa na daidaito, mutunta juna da moriyar bangarorin biyu.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar tsaro a nahiyar Afrika, musamman a yankin Sahel da ke fuskantar barazanar kungiyoyin ta’addanci da rashin zaman lafiya.
Shugaban na Türkiye ya ce ƙasarsa na tsaye tare da ƙawayenta da ƙasashen da take da dangantakar ‘yan uwantaka da su wajen yaƙi da ta’addanci da ƙarfafa zaman lafiya a yankin.
