Sport
Dollar
40,4240
0.06 %Euro
47,3842
0.07 %Gram Gold
4.409,0700
-0.05 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede ya ce duk gwamnan da aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bayan ƙarewar wa'adinsa.
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa gwamnoni 18 daga cikin 36 da ke kan mulki a halin yanzu suna fuskantar bincike daga hukumar.
Olukoyede ya ce duk waɗanda aka samu da laifi za su fuskanci hukunci bayan karewar wa'adinsu. Ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai da aka shirya don masu shirya fina-finai, mawaƙa, da ‘yan canji, wanda aka gudanar a birnin Legas a ranar Juma’a.
Taron ya mayar da hankali ne kan wayar da kai game da illar lalatawa da kuma raina kuɗin naira.
“Yayin da nake magana da ku yanzu, ina binciken kusan gwamnoni 18 da ke kan mulki. Bayan sun bar ofis, za mu ɗauki mataki na gaba,” in ji Olukoyede.
Sai dai bai ambaci sunayen gwamnonin da ake bincike ba, kuma bai fayyace cikakkun bayanai game da binciken ba.
Tun bayan kafa hukumar EFCC, ta tuhumi fiye da gwamnoni 30 a ƙasar inda har wasu suka zauna a gidan yari.
Ko a shekarar 2024, sai da EFCC ɗin ta tuhumi gwamnoni biyar da cin hanci waɗanda suka haɗa da tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello da tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed da tsohon gwamnan Anambra Willie Obiano da tsohon gwamnan Taraba Darius Ishaku da tsohon gwamnan Abia Theodore Orji.
Comments
No comments Yet
Comment