Dollar

40,4234

0.06 %

Euro

47,3605

0.06 %

Gram Gold

4.409,0700

-0.05 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Jangebe da ke Zamfara, inda a garin ne aka taɓa sace mata 'yan makarantar sakandare fiye da 300 a 2021.

'Yan bindiga sun kashe manoma tara, sun sace 15 a Jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe manoma tara a ranar Juma’a a jihar Zamfara, tare da garkuwa da su mutane.

Lamarin ya faru ne a wajen ƙauyen Jangebe, cikin karamar hukumar Talata Mafara, inda ‘yan bindigar da ke kan babura suka kewaye manoman da ke aikin gona, suka hallaka tara daga cikinsu, sannan suka sace fiye da mutum 15, kamar yadda wata majiya daga yankin ta tabbatar da hakan.

Wani jagoran siyasa na yankin Talata Mafara, Yahaya Yari Abubakar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: “‘Yan bindiga sun kai wa manoman hari, inda suka kashe tara daga cikinsu.”

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa ‘yan bindigar sun ɗauki lokaci suna zagaye gonakin kafin su kai harin, kuma sun tafi da wasu daga cikin manoman da suka kama.

A fadin Nijeriya, ‘yan bindiga sun mamaye yankunan karkara, musamman a arewa maso yamma da tsakiyar ƙasar, sakamakon talauci da sakacin gwamnati, inda suke yi wa jama’a fashi, kona ƙauyuka, karɓar haraji da kuma satar mutane don neman kudin fansa.

‘Yan bindigar, waɗanda suka zo a kan babura, sun kai harin ne a lokacin da manoman ke aikin gona. An bayyana cewa har yanzu ba a ji komai daga waɗanda suka yi garkuwa da su ba.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da shugaban kungiyar sa-kai ta ƙauyen Jangebe da abokan aikinsa guda biyar, tare da mazauna ƙauyen guda uku, in ji wani mazaunin yankin, Abu Zaki.

Wani mazaunin ƙauyen, Bello Ahmadu, ya ce: “Kowa yanzu yana tsoron zuwa gona saboda fargabar harin ‘yan bindiga.”

A Jangebe ne dai 2021 aka sace fiye da ‘yan mata 300 daga wata makarantar kwana – daya daga cikin satar dalibai mafi girma a tarihin Nijeriya.

An saki matan ne bayan hukumomi sun biya kuɗin fansa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#