Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Gwamnatin Jihar Legas ta ce an sanar da ita a hukumance game da bayanin da Adichie ta bayar kan lamarin, wanda ta bayyana a matsayin abin matuƙar tayar da hankali da baƙin ciki.
Gwamnatin Jihar Legas ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin sakaci a fannin lafiya da ake zargin ya yi sanadin mutuwar Nkanu Nnamdi mai watanni 21, ɗan shahararriyar marubuciya Chimamanda Ngozi Adichie, a wani asibiti mai zaman kansa a jihar.
Yaron, wanda yake ɗaya daga cikin ’yan tagwaye na Adichie, rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Gwamnatin Jihar Legas ta ce an sanar da ita a hukumance game da bayanin da Adichie ta bayar kan lamarin, wanda ta bayyana a matsayin abin matuƙar tayar da hankali da baƙin ciki.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba Gwamna Shawara Ta Musamman Kan Harkokin Lafiya, Dakta Kemi Ogunyemi, ta saka wa hannu, gwamnatin Legas ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan, inda ta jaddada cewa rasuwar yaro babban bala’i ne mai matuƙar taɓa zuciya.
Gwamnatin jihar ta sake tabbatar da matsayinta na rashin lamuncewa ko kaɗan kan sakaci a fannin lafiya da kuma rashin ƙwarewa a kowace cibiyar lafiya da ke aiki a fadin Jihar Legas.
Ta bayyana cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya umarci Hukumar Kula da Asibitoci da Tantancewa (HEFAMAA) da ta ƙaddamar da cikakken bincike mai zaman kansa nan take a kuma yanayi na gaskiya kan musababbin mutuwar yaron.
A cewar sanarwar, HEFAMAA ta riga ta ziyarci asibitin da lamarin ya faru tare da fara cikakken nazari kan dukkan zarge-zarge da rahotannin da suka shafi lamarin.
Binciken zai kuma gudana ne tare da haɗin gwiwar Majalisar Kula da Ayyukan Likitoci ta Nijeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa.
Gwamnatin ta ce binciken zai duba bin ka’idojin aikin asibiti, ɗabi’ar ƙwararru, ƙa’idojin tsaron marasa lafiya, da rawar da kowane ɓangare ya taka.
Comments
No comments Yet
Comment