Sport
Dollar
43,1631
0.11 %Euro
50,3632
0.06 %Gram Gold
6.412,3600
0.7 %Quarter Gold
10.547,9300
0.43 %Silver
122,8200
4.02 %Rahoton Q3 na 2025 ya bayyana cewa jimilla hatsarin da ke da alaka da lantarki 57 ne ya afku a fadin kasar a wannan lokaci.
Alkaluman baya bayan nan game da lantarki da Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya ta fitar sun bayyana mutuwar mutum 33, yayin da wasu 33 kuma suka jikkata sakamakon hatsarin da ke da alaa da lantarki a fadin kasar.
Rahoton Q3 na 2025 ya bayyana cewa jimillar hatsarin da ke da alaka da lantarki 57 ne ya afku a fadin kasar a wannan lokaci.
An samu hatsari a wurare daban-daban, inda cibiyoyin lantarki na Ikeja da Kano ke da mafi yawan hatsarin a watanni uku na ukun 2025.
Dukkan yankunan biyu sun fuskanci hatsari sau 10. Sannan Ikeja ta fuskanci rasa rayuka hudu da jikkatar mutum shida, sai Kano da ta samu asarar rayuka 6 da jikkatar mutum hudu.
A yayin da Abuja, Jos, Aba, Port Harcourt, Enugu da Yola suka fuskanci hatsari daban-daban, Eko, Kaduna da TCN ma sun shiga jerin. Aan samu raunuka sosai daga cikin hadarurrukan.
An bayyana cewa rashin bin ka’idar aiki da mummunan yanayi ne suka janyo mafi yawan hadurran da ma yawaitar jikkata, inda tsinkewa da fitar waya suka janyo mutuwar mutane 10 da jikkatar wasu 7.
An alakanta mutuwa 10 da jikkata 18 ga sakacin aikin da rashin bin ka’ida, inda aka samu kuskuren ma’aikata, rashin daukar matakan kariya da suka kamata da rashin ma’aikatan da ke da lasisin yin aikin.
Shiga wuraren da kayan wuta suke ba tare da izini ko ta barauniyar hanya ma sun janyo afkuwar hadurran, inda aka samu jikkatar mutane uku a wannan lokaci.
Barna ba ta janyo hatsari da yawa ba, amma kuma ta janyo mutuwar mutane biyu.
A nata bangaren, Hukumar ta NERC ta ce ta fara gudanar da bincike kan dukkan hatsarin d aaka rawaito ya afku da ma kayan da suka fashe, kamawar gobara da ayyukan barna a watanni ukun.
Hukumar gudanarwar ta kuma kara da cewa ta shirya taron masu ruwa da tsaki da ke da manufar inganta hanyoyin kariya a cibiyoyin, inda aka tattara jami’an lafiya da bayar da kariya daga kamfanonin lantarki don duba hadurran da suka afku, su bayyana kwarewarsu da darussan da aka dauka, sannan su samar da hanyoyin inganta yanayin da ake ciki.
A rahoton Q2 da aka fitar an bayyana samun hatsari 60 a cibiyoyin lantarki, an samu jikkatar mutane 19.
Comments
No comments Yet
Comment