Dollar

43,1623

0.1 %

Euro

50,2905

-0.08 %

Gram Gold

6.394,7300

0.43 %

Quarter Gold

10.547,9300

0.43 %

Silver

123,2200

4.36 %

Wata kotun majistare a Hadejia da ke Jihar Jigawa, ta bayar da umarnin kamawa tare da binciken jami’in bayan zargin cewa ya sace wata yarinya ’yar shekara 16, ya tsare ta ba bisa ƙa’ida ba, sannan ya tilasta mata sauya addini.

Hukumar DSS a Nijeriya ta tabbatar da kama ma'aikacinta kan zargin sace ƙaramar yarinya a Jigawa

 Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta mayar da martani kan zargin da ake yi cewa ɗaya daga cikin ma’aikatanta ya sace tare da lalata da ƙaramar yarinya.

Wata kotun majistare a Hadejia da ke Jihar Jigawa, ta bayar da umarnin kamawa tare da binciken jami’in bayan zargin cewa ya sace wata yarinya ’yar shekara 16, ya tsare ta ba bisa ƙa’ida ba, sannan ya tilasta mata sauya addini.

Lamarin ya samo asali ne daga wani ƙorafi da wani lauya, Gamji Lawchain, ya shigar a madadin mahaifin Walida Ibrahim wadda it ace yarinyar.

A cikin ƙorafin, an zargi jami’in da sace Walida fiye da shekaru biyu da suka wuce, ya tsare ta ba bisa ƙa’ida ba, ya yi lalata da ita, sannan ya tilasta mata sauya addininta daga Musulunci zuwa Kiristanci ba tare da izinin iyayenta ba.

Haka kuma, ƙorafin ya bayyana cewa ta haifi ɗa yayin da take ƙarama.

Masu shigar da ƙorafin sun yi Allah wadai da cin zarafin, tare da kira da a gaggauta dakatar da jami’in, a kama shi, a gurfanar da shi, sannan a gudanar da bincike mai zaman kansa kan ofishin DSS da ke Karmajji.

Lauyoyin sun jaddada mummunan halin damuwar da aka jefa iyalan Walida a ciki, inda suka ce tsawon damuwar da suka shiga ya taimaka wajen rasuwar mahaifiyarta.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 9 ga Janairun 2026, Favour Dozie, Mataimakiyar Darakta Mai kula da Hulɗa da Jama’a a Hedkwatar DSS ta ƙasa, ta tabbatar da cewa ana ci gaba da binciken lamarin, tare da tabbatar da cewa za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

Ta kuma bayyana cewa sunan jami’in da ake zargi shi ne Ifeanyi Onyewuenyi, ba Ifeanyi Festus ba kamar yadda aka ambata a cikin ƙorafin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#