Dollar

43,1606

0.1 %

Euro

50,3047

-0.06 %

Gram Gold

6.397,4500

0.47 %

Quarter Gold

10.547,9300

0.43 %

Silver

123,3800

4.49 %

Wannan harin na zuwa ne mako guda kacal bayan ’yanbindiga sun kashe mutum 42 a wasu ƙauyukan jihar, ciki har da kasuwar Daji da ke kauyen Demo, a Borgu da kuma Kananan Hukumomin Agwara da ke makwabtaka da ita.

'Yan bindiga sun kashe mutum huɗu a wani sabon hari da suka kai Jihar Neja

’Yanbindiga sun kai hari kauyen Damala da ke gundumar Woko a Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, inda suka kashe aƙalla mutane huɗu.

Harin, wanda ya faru da safiyar Asabar, 10 ga Janairu, ya zo ne mako guda kacal bayan ’yanbindiga sun kashe mutum 42 a wasu ƙauyukan jihar, ciki har da kasuwar ⁠Daji da ke kauyen Demo, a Borgu da kuma Kananan Hukumomin Agwara da ke makwabtaka da ita.

Rundunar ’Yansandan Nijeriya Reshen Jihar Neja ta tabbatar da sabon harin ga gidan talabijin na Channels a Nijeriya a ranar Lahadi.

A cikin wata sanarwa, Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce maharan sun afka ƙauyen, sun sace adadin shanu da ba a bayyana ba, tare da kashe mazauna huɗu a yayin harin.

Ya ce ’yanbindigar sun kuma ƙona shaguna da dama a cikin al’ummar kafin su tsere daga wurin.

Abiodun, wanda ke da mukamin Sufurintendan ’Yansanda, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun gaggauta mayar da martani kan lamarin kuma sun ziyarci yankin da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da aikin sinitiri domin kawar da barazana daga yankin, tare da ƙarfafa sa ido na tsaro domin hana ƙarin hare-hare da tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Kakakin rundunar ya tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da ƙoƙari domin kama masu aikata laifin da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#