Sport
Dollar
41,8410
0.03 %Euro
48,7015
0.15 %Gram Gold
5.615,6900
0.83 %Quarter Gold
9.360,7700
0 %Silver
69,9600
1.07 %Rahotanni sun ce magoya bayan Kano Pillars sun garzaya cikin filin wasan Sani Abacha Stadium ne suka ci zarafin lafari da ‘yan wasan Shooting Stars bayan ƙungiyar ta farke ƙwallon da aka zura mata a minti na 94 inda suka tashi da ci 1-1.
Manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa, ya nemi afuwa daga ‘yan wasa da masu horrarwa da magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Shooting Stars ta Ibadan da alƙalan wasa kan hargitsin da aka yi a wasan da suka tashi canjaras a Kano.
Ahmed Musa wanda ke taka leda a ƙungiyar ta Kano Pillars ya kuma nemi afuwar duk wani masoyin ƙwallon ƙafa a ƙasar da ya ji haushin yadda aka yi bayan an gama wasan.
“Na san zafin irin wannan abin mai lalata wasanmu. A yi haƙuri sosai. Tashin hankali ba shi da gurbi a ƙwallon ƙafa. Ba za a lamunce shi ba, ba za a iya samar masa hujja ba kuma ya saɓa wa duk abin da aka san wannan wasa mai kyau da shi,” in ji Ahmed Musa a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
Rahotanni sun ce magoya bayan Kano Pillars sun garzaya cikin filin wasan Sani Abacha Stadium ne suka ci zarafin lafari da ‘yan wasan Shooting Stars bayan ƙungiyar ta farke ƙwallon da aka zura mata a minti na 94 inda suka tashi da ci 1-1.
“Ana wasan ƙwallon ƙafa ne domin haɗa kai da zaburar da juna da kuma ƙayartawa. Idan ya koma wani wurin hargitsi da cutarwa, ya zama wajibi kada mu ɗauke ido daga gare shi, dole mu fuskance shi,” in ji ɗan wasan da ke buga wa tawagar Nijeriya ta Super Eagles.
Kazalika Ahmed Musa ya ce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars za ta yi aiki sahu da ƙafa da hukumomi masu ruwa da tsaki domin gano waɗanda suka yi “wannan abin kunya.”
“Mun san cewa ba da haƙuri kawai bai isa ba. Dole a ɗauki mataki. Za ɗauki babban mataki a cikin gida domin tabbatar da cewa irin wannan abin bai sake faruwa ba,” in ji shi.
Ahmed Musa ya bayyana wa magoyan baya Masu Gida cewa ƙungiyar tana alfahari da tarihinta da magoya bayanta.
“Amma ba da tashin hankali ake nuna goyon baya ba, sai ta hanyar girmamawa da kishi da kuma kai zuciya nesa. Dole wannan ya kasance wani lokaci na sauyi a gare mu. Dole mu tuna wa duniya cewa za mu iya yi wa wannan ƙungiyar gagarumar soyayya ba tare da lalata komai ba,” in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment