Dollar

41,8477

0.02 %

Euro

48,6377

0.04 %

Gram Gold

5.570,3600

0.02 %

Quarter Gold

9.360,7700

0 %

Silver

69,2400

0.02 %

Wakilin tauraron ɗan wasan Barcelona, Robert Lewandowski ya yi jawabi kan makomar ɗan wasan mai shekaru 37.

Ko Lewandowski ya kama hanyar barin Barcelona?

Rahotanni daga Barcelona na cewa ƙungiyar ta yi watsi da tattaunawar da take da tauraron ɗan wasa Robert Lewandowski, kan tsawaita kwantiraginsa.

Wannan labari ya sanya masoya Barca sun fara tararrabi kan makomar Lewandowski a ƙungiyar, yayin da ake shiga watannin ƙarshe na kwantiraginsa.

Ana cikin wannan ne sai ga Pini Zahavi, wakilin ɗan wasan yana bayanin cewa ba zai iya fitar da rai daga yiwuwar Lewandowski ya bar Barca ba.

Tun bayan zuwan sabon kocin Barca, Hansi Flick a bara ake maganganu kan makomar ɗan wasan, kasancewar yana cikin masu yawan shekaru a tawagar.

Fifita matasa

Raɗe-raɗi kan ɗan wasan ɗan asalin Poland na cewa Barcelona ta karkata kan zaɓin ƙin sabunta kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 37, wadda za ta ƙare a ƙarshen kakar nan.

Sai dai kuma, wasu rahotanni na cewa wakilin ɗan wasan yana iƙirarin cewa ba a kammala yanke hukunci kan makomar Lewandowski ba.

Tun bayan zuwansa a 2022, Robert Lewandowski ya ciyo wa Barcelona ƙwallaye 105 a wasanni 156, duk da cewa a baya bayan nan bai buga mintunan wasanni da dama ba.

Masu nazarin ƙwallo musamman a Barcelona, suna ganin ƙungiyar tana mai da hankali kan gina matasan ‘yan wasa ne, maimakon dogaro kan dattijai irin su Lewandowski.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#