Dollar

42,8585

0.06 %

Euro

50,8450

0.17 %

Gram Gold

6.219,6700

0.43 %

Quarter Gold

10.205,2300

0 %

Silver

98,9500

0.45 %

Shugaban hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ya ce sauyin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ganin gasar ta dace da jadawalin ƙasashen duniya.

AFCON: Za a riƙa yin Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka bayan shekara huɗu daga 2028

Shugaban hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) Patrice Motsepe ranar Asabar ya ce daga shekarar 2028 za a riƙa gudanar da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka bayan shekara huɗu-huɗu.

Motsepe ya ce hakan wani ɓangare ne na gagarumin sauyin da suke burin kawowa a fagen ƙwallon ƙafar Afirka domin ya dace da jadawalin ƙasashen duniya.

Gudanar da gasar AFCON bayan shekaru biyu-biyu yana samar wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Afirka kuɗin shiga, amma Motsepe ya ce ƙaddamar da gasar lig ta ƙasashen Afirka - wadda take kama da gasar UEFA - za ta taimaka wajen sama wa ƙasashen kuɗin shiga.

"Babban abin da ke gabanmu a yanzu shi ne gasar AFCON amma daga shekarar 2027 za mu je Tanzania, Kenya da Uganda, kuma gasar AFCON ita ce wadda za a yi a 2028," a cewar Motsepe a hira da manema labarai a birnin Rabat na ƙasar Maroko, a yayin da ake shirin soma gasar cin kofin ƙasashen Afirka, wato AFCON 2025.

Damar ɗaukar nauyin gasar

Ya ƙara da cewa za a bayar da damar ɗaukar nauyin gasar ga ƙasashen da ke sha’awar karɓar baƙuncin Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka ta 2028.

"Bayan Gasar Duniya ta FIFA ta Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa a 2029 za mu gudanar da gasar farko ta lig ta ƙasashen Afirka ... inda za a saka ƙarin kuɗaɗe da kayan aiki da fafatawa a gasar.

"A wani ɓangare na shirin yin gasar, za a riƙa gudanar da gasar AFCON bayan shekara huɗu-huɗu."

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#