Za a ƙara kwanaki 10 ne don bai wa masu zuba jari daga sauran ƙasashen Afirka damar sayen hannayen jari a matatar, a cewar wani babban jami'in kamfanin kuma mai ba da shawara.
Za a ƙara kwana 10 a wa’adin sayar da hannun jarin matatar man Dangote ga jama’a (IPO), domin bai wa masu zuba jari daga wasu ƙasashen Afirka damar shiga cikin shirin, kamar yadda wani babban jami’in kamfanin kuma mai ba da shawara kan sayar da hannayen jarin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
An buɗe shirin sayar da hannun jarin ne kimanin wata guda da ya gabata, kuma an tsara rufe shi a ranar Talata. Ana sa ran tara kuɗi har dala biliyan 2.1 daga jama’a domin faɗaɗa matatar, a wani cinikin hannun jari da ake sa ran zai zama mafi girma da aka taɓa gudanarwa a Afirka.
Matatar, ta Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, na neman ƙara yawan masu sa hannun jari a katafaren kamfanin tace mai da ke da ƙarfin tace ganga 700,000 a kowace rana. Shirin ya shafi sayar da hannun jari ga masu zuba jari har miliyan 10 a Nijeriya da sauran ƙasashen nahiyar Afirka.
Wani mai ba da shawara kan cinikin ya ce za a fitar da sanarwa a hukumance kan ƙarin wa’adin daga baya a ranar Litinin.
Hukumar Kula da Kasuwannin Hannun Jari ta Nijeriya (SEC) da kuma kamfanin gudanar da kasuwar hannun jari ta NGX Group ba su bayar da wani martani nan take ba. Shi ma mai magana da yawun kamfanin Dangote ya ƙi yin tsokaci kan batun.
