Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ɗanwasan Tottenham ɗan asalin Ivory Coast, Yves Bissouma ya yi asarar sama da fam dubu ɗari takwas daga asusunsa na banki.
Wani ɗan damfara ya kwashe wa ɗanwasan Tottenham, Yves Bissouma sama da fam £800,000 daga asusunsa na banki a Ingila.
Lamarin ya faru ne yayin da aka kwashe masa kuɗi daga asusun banki ta haramtacciyar hanya ba tare da sanin sa.
Rahotanni na cewa Bissouma mai shekaru 29, ɗan wasan tsakiya a Tottenham, ya rasa kuɗaɗen ne tsakanin Satumban 2022 da yunin 2024.
Tuni an kama wanda ake zargi da aikata damfarar, mai suna Maurice Gomes, mai shekaru 31, bayan Bissouma ya kai ƙorafi gun ‘yan-sanda.
Hukumar ‘yansandan London Metropolitan ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an caji Gomes da laifuka biyu na "zamba da amfani da hanyar bogi".
An kwashe kuɗaɗen ne daga asusun bankin Bissouma da ke bankin VIP, wani banki da ya shahara wajen taurari da biloniyoyi da mambobin gidan sarautar Burtaniya.
Ana sa ran Bissouma zai bayyana gaban kotun majistire ta Highbury Corner ranar 7 ga Nuwamba, don ba da shaida.
A 2024 ma an taɓa sace wa Yves Bissouma agogon alfarma da ya kai fam dubu 255, lokacin da ya je hutu birnin Cannes na Faransa.
Comments
No comments Yet
Comment