Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ministan Kuɗi na Nijeriya Wale Edun, ne ya bayyana amincewar da aka yi na cin bashin inda ya ce za a yi amfani da shi wurin tallafa wa mutanen da rikici ya raba da muhallansu da kuma aikin aiwatar da inganta cibiyoyin kiwon lafiya a Jihar Sokoto.
Gwamnatin Nijeriya ta amince da cin bashi daga ƙasar waje wanda yawansa ya kai dala miliyan 396 domin tallafa wa mahimman shirye-shiryen jinƙai da kiwon lafiya a arewacin Nijeriya.
Ministan Kuɗi na Nijeriya Wale Edun ne ya bayyana amincewar da aka yi na cin bashin yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.
Edun ya ce bashin na farko shi ne bashi na dala miliyan 300 daga Babban Bankin Duniya domin tallafa wa mutanen da rikici ya raba da muhallansu da al’ummomin da suka karɓi baƙuncin mutanen a jihohi da dama na arewacin Nijeriya.
Ya ƙara bayyana cewa amincewar ta biyu ta haɗa da bashi na haɗin gwiwa na dala miliyan 96 daga Bankin Raya Musulunci (IsDB) da Bankin Raya Afirka (AfDB) — dala miliyan 50 daga IsDB da dala miliyan 46 daga AfDB.
Za a yi amfani da kudin ne domin aiwatar da aikin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a Jihar Sokoto, inda Gwamnatin Jihar Sokoto za ta bayar da gudunmawarta ita ma.
“Bashin dala miliyan 300 daga Babban Bankin Duniya yana nufin tallafa wa mutanen da rikici ya raba da muhallansu da kuma jihohin al’ummomin da ke karɓar su a jihohi daban-daban na Arewa.
“Na biyu kuma bashi ne daga Bankin Raya Musulunci da Bankin Raya Afirka, jimillar dala miliyan 96, domin aikin gina cibiyoyin kiwon lafiya a Sokoto,” in ji Edun.
Ministan ya bayyana cewa waɗannan ayyuka suna da matuƙar muhimmanci ga Shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu, wanda ke da nufin magance bambance-bambancen yankuna, inganta samun damar kiwon lafiya, da kuma farfaɗo da al’ummomin da rikice-rikice suka shafa.
Edun ya kuma gabatar wa majalisar rahoto kan halin tattalin arzikin ƙasa, inda ya ce sabbin bayanai sun nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun sauyi mai kyau sakamakon gyare-gyaren da aka yi a fannin kuɗi da tsare-tsaren kuɗaɗe.
Comments
No comments Yet
Comment