Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Israila ta kashe kusan mutane 69,000, mafi yawancin su mata da yara, kuma ta jikkata wasu 170,600 a kisan ƙare-dangi a Gaza tun daga Oktoba 2023.
Turkiyya ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da wasu mutane 36 bisa zargin rawar da suka taka a “kisan kare dangi” a yankin Gaza na Falasɗinu.
Ofishin Babban Mai Shigar da Ƙara na Istanbul ya bayyana a ranar Jumma’a cewa ya bayar da sammacin kama mutane 37, ciki har da Benjamin Netanyahu, Israel Katz, Eyal Zamir, da David Saar Salama, bisa zargin aikata “kisan kare-dangi” a Gaza.
A watan Nuwamban bara, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta bayar da sammacin kama Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant bisa zargin aikata laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil’adama a Gaza.
Haka kuma, Isra’ila tana fuskantar shari’ar kisan kare dangi a Kotun Duniya (ICJ) dangane da yakin da take yi a yankin Gaza.
Comments
No comments Yet
Comment