Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugabannin kasashe masu matsakaici da karancin tattalin arziki sun yi kira don daukar karfafan matakai, yayain da shugaban Syria al Sharaa ya yi kira ga kasashe su saka jari a ayyukan inganta muhalli.

COP30: Manyan masu gurbata muhalli na duniya ba su je taron sauyin yanayi na Brazil ba

Daruruwan ministoci da shugabannin kasashe da gwamnatoci, ciki har da na Spain, Jamus, da Namibia, sun taru a Belem, Brazil, don ci gaba da taro a ranar Jumma’a, gabanin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya na tsawon makonni biyu, COP30, wanda za a fara a ranar Litinin.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, tare da wasu shugabannin kasashe, sun bayyana a ranar Alhamis cewa duniya ba za ta iya dakatar da dumamar yanayi kasa da 1.5C ba, wanda shi ne babban burin yarjejeniyar Paris da aka sanya shekaru goma da suka gabata. Sai dai sun ce har yanzu ba su daina fatan cim ma burin da suke hankoro ba na 2C.

Rashin halartar shugabannin kasashen da suka fi gurbata muhalli, ciki har da Amurka, inda Shugaba Donald Trump ke yin watsi da ilimin yanayi a matsayin “karya,” ya yi tasiri a tattaunawar, amma hakan ya kuma kara karfafa kira ga karin hadin kai da daukar mataki.

Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya yi kira a jawabin bude taron don samar da “taswirar hanya” don dakatar da sare dazuzzuka, rage dogaro da man fetur, da kuma tara kudaden da ake bukata don cim ma wadannan manufofi, wanda ya samu karbuwa a wajen mahalartan.

Kungiyar da ke goyon bayan kiran Lula ta hada da kananan tsibiran da ke fuskantar barazana ta tsanantuwar mahaukaciyar guguwa da kuma hauhawar matakin teku, wanda ke barazana ga rayuwarsu.

Ga abin da shugabannin wasu kasashe masu karamin karfi da matsakaici suka fada gabanin taron.

Syria ta yi kira ga zuba jari a makamashin da ake sabuntawa

Shugaban Syria, Ahmed al Sharaa, ya yi kira ga zuba jari na kasa da kasa a bangaren makamashin da ake sabuntawa da ci gaban birane masu dorewa a Syria, yana mai jaddada kudurin kasarsa na sake gina kasa daidai da manufofin duniya kan yanayi.

Da yake jawabi a taron shugabannin COP30, Sharaa ya ce Syria ta fuskanci “kalubale masu tsanani na muhalli a cikin ‘yan shekarun nan, wadanda tasirinsu ya taru kan mutane da albarkatu,” wanda ya kara ta’azzara saboda rikici da kuma matsugunin ‘yan gudun hijira da ya kara matsa lamba kan albarkatun da tuni suka yi karanci.

Ya lura cewa Syria ta sha fama da fari mafi tsanani cikin shekaru fiye da 60 a bana, yana bayyana hakan a matsayin shaida ta “kololuwar” tasirin rikicin yanayi kan kasar.

“Manufarmu mai cike da buri tana bayyana a cikin shirye-shiryen sake gina kasa da farfado da tattalin arziki, wanda muka fara aiwatarwa da fassara zuwa manufofi, shirye-shirye, da ayyuka masu amfani,” in ji shugaban.

“Shi ya sa muke gayyatar ku don zuba jari a Syria — a bangarori kamar makamashi mai sabuntawa, birane masu dorewa, da kuma manyan ayyukan zuba jari da ke samun kariya, tallafi, da tabbaci daga gwamnati.”

Kananan tsibiran duniya: ‘Kungiyar masu himma’

A taron, Mia Mottley, firaministar Barbados, daya daga cikin kananan tsibiran da suka fi fuskantar barazana daga hauhawar matakin teku da abubuwan da suka shafi yanayi kamar guguwar iska da mahaukaciyar guguwa, ta ce: “Abokaina, duniya ba ta taba samun sauyi daga masu kallo da masu sukar lamari ba.”

Mottley tana mayar da martani ne kan yadda Trump ya rage darajar rikicin yanayi.

“Shin muna bukatar kowa ya dauki mataki a lokaci guda? Hakan zai fi kyau. Amma idan ba mu samu ba, to dole ne mu gina wata kungiya ta masu niyya kuma mu nuna wa kowa abin da za su amfana,” in ji Mottley.

Ta kuma yi kira ga duniya da ta “ja birki kan methane,” wani “babban gurbataccen abu” da kuma babban sinadarin iskar gas na halitta, wanda ke da saukin zubewa daga bututun iskar gas da wuraren da ake sarrafa shi.

Firaministan Antigua da Barbuda, Gaston Browne, wanda kasarsa ta kasance karamin tsibiri mai kasa da ke fuskantar barazana, ya soki “manyan masu gurbata muhalli (wadanda) ke ci gaba da lalata muhallin teku da na kasa tare da gurbatattun iskar gas na man fetur.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#