Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Mamdani, wanda iyayensa ‘yan asalin Indiya ne da aka haifa a Uganda amma suka koma New York, ya zama Musulmi kuma ɗan asalin nahiyar Asiya na farko da ya lashe zaɓen Magajin Birnin.
Mazauna birnin New York sun zaɓi Zohran Mamdani, wani matashi Musulmi kuma “mai ra’ayin gurguzu” ɗan jam’iyyar Democrat a matsayin Magajin Birnin New York yayin da Amurkawa suka fara ƙada ƙuri’a a karon farko a wa’adin Trump na biyu mai cike da hayaniya a zaɓukan ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.
Mamdani ya kayar da tsohon gwamna Andrew Cuomo, wani ɗan jam’iyyar Democrat da ya yi takara a matsayin indipenda bayan ya sha kaye a zaɓen fid da gwani.
Curtis Sliwa, ɗan takarar Jam’iyyar Republic kuma wanda ya kafa ƙungiyar sa-kai ta Guardian Angels mai hana aikata laifuka, ya ƙarƙare a matsayi na uku.
"Mataki na gaba kuma mataki na ƙarshe shi ne Ma’aikatar Magajin Gari," kamar yadda Mamdani ya bayyana a wani bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X bayan an bayyana nasararsa.
Mamdani, mai shekara 34, ya bayyana kansa a matsayin ɗan gurguzu wanda ba a san da shi ba kafin ya yi nasarar ba-zata a zaɓen fid da gwani.
Ya mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa ga mazauna Birnin New York inda ya gina goyon baya ta hanyar ganawa da mutane ɗaya bayan ɗaya da kuma amfani da bidiyon da ya dace da shafukan sada zumunta da ke nuna shi yana tafiya a kan titunan birnin kuma yana magana da masu ƙada ƙuri’a.
Da samun wannan nasarar, Mamdani, wanda iyayensa ‘yan asalin Indiya da suka haifa a Uganda kuma suka rene shi a New York tun yana mai shekara bakwai da haihuwa, ya zama Musulmi kuma ɗan nahiyar Asiya na farko da ya zama Magajin Birnin na New york.
Ya samu nasara ce duk kuwa da zazzafar suka da ya sha daga Shugaba Donald Trump da manyan attajirai da kafafen watsa labarai na masu ra’ayin riƙau game da manufofinsa da tarihinsa na Musulunci.
A wani mataki na amfani da ƙabilanci ba tare da kunya ba, Trump ya bayyana Mamdani ranar Talata a matsayin "wanda ya tsani Yahudawa."
"Duk wani Bayahude da ya zaɓi Zohran Mamdani, wanda ya bayyana da bakinsa cewa ya TSANI YAHUDAWA, daƙiƙi ne!!!" kamar yadda shugaban ƙasar ɗan Jam’iyyar Republican ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social.
Manyan attajirai ciki har da Bill Ackman sun soki Mamdani kuma sun ba da kuɗaɗe ga abokan hamayyarsa, yayin da kafafen watsa labarai masu ra’ayin riƙau ciki har da kafar The New York Post sun buga labarai mara daɗi game da yaƙin neman zaɓensa.
Yaƙin neman zaɓen ya mayar da hankali ne kan tsadar rayuwa da laifuka da kuma yadda ko wane ɗan takara zai yi da Trump, wanda ya yi barazanar hana New York kuɗi daga gwamnatin Tarayya.
Mamdani ya mayar da hankalin yaƙin neman zaɓensa kan samun sauƙin rayuwa.
Manufofinsa sun haɗa da dakatar da ƙara kuɗin hayar gidaje da hawa motocin bas kyauta da lura da yara ga kowa da kuma shagunan sayar da cefane da gwamnatin birnin za ta buɗe a farashi mai rahusa.
Manufofinsa sun haɗa da ƙara haraji kan attajirai da suka fi kuɗi a Birnin New York da kuma ƙara haraji kan kamfanoni, lamarin da ya ƙara fargaba tsakanin masu kuɗi cewa tagomashin birnin zai ragu.
Ɗaukakar Mamdani mai cike da ban mamaki ta nuna wani gagarumin sauyi a Jam’iyyar Democrat bayan gazawar masu ra’ayin tsaka-tsaki da masu ra’ayin ‘yan-mazan-jiya.
Kazalika, nasarorin Jam’iyyar Democrat a zaɓen gwamnan jihohin Virginia da New Jersey ta nuna wani sauyi a fagen siyasa yayin da ƙasar ke fuskantar zaɓen tsakiyar wa’adi na shekara mai zuwa lokacin da za a iya samun iko kan majalisar dokokin ƙasar.
Sai dai kuma Trump ya alaƙanta kayen da Jam’iyyar Republican ta sha a biranen New York da New Jersey da kuma Virginia ga rashin bayyanar sunansa a kan ƙuri’u da kuma toshe aljihun gwamnatin tarayyar da ƙasar ke fama da shi.
A birnin New Jersey, ɗan takarar Jam’iyyar Democrat Mikie Sherrill ya doke wani ɗan kasuwa da Trump ya goya wa baya kuma a Jihar Virginia, ‘yar takarar Jam’iyyar Democrat Abigail Spanberger ta yi nasara a zaɓen gwamna inda ta kayar da Jam’iyyar Republican.
Comments
No comments Yet
Comment