Tuni aka fara gina dandalin mai suna “Memorial FC Barcelona” tare da haɗin-gwiwar kamfanin binne gawa na Més Que Un Memorial SL, da nufin jaddada alaƙar ƙungiyar mai farin jini, da ɗumbin masoyanta.
Yayin da Barcelona ke neman kuɗin-shiga ido-rufe, ƙungiyar ta fara bai wa masoyanta damar su biya kuɗi don samun gurbin da za a kafa allon tunawa da su da adana tokar gawarsu idan sun mutu, a wani sashe na filin wasanta.
Barca ta sanar da ware wani yanki na filin wasanta na Camp Nou, ‘yan mitoci kaɗan daga filin ƙwallo, don ya zama wajen tunawa da mamata masoyan Barca.
Tuni aka fara gina dandalin mai suna “Memorial FC Barcelona”, tare da haɗin-gwiwar kamfanin binne gawa na Més Que Un Memorial SL, da nufin jaddada alaƙar ƙungiyar mai farin jini, da ɗumbin masoyanta.
Wannan shiri wata alama ce da ke nuna yadda Barcelona take girmama masoyanta, wadanda a yanzu za su samu damar ajiye tarihinsu a filin wasanta.
Ba sai lallai mutum ya kasance mamban ƙungiyar masoyanta ba, wanda ba mamba ba ma daga ko’ina a duniya zai samu wannan dama.
Mutum na da zaɓin biyan kuɗi a saka allon tunawa da shi, ko tunawa da wani makusancinsa. Za a rubuta sunan mamacin da kuma saƙo na musamman don tunawa da shi.
Tuni tarin masoyan Barcelona suka fara nuna sha’awar shiga shirin, ciki har da tsaffin ‘yanƙwallo da ‘yan-uwansu.
Akwai zaɓin biyan kuɗin adana allon tunawar na tsawon shekaru 10, 25, ko 50, kuma mutum na da zaɓin faɗar gurbin da yake so. Amma adana tokar gawar mutum zaɓi ne ba na dole ba.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Reuters (Wire)

