Kwararrun masu aikin fassara a Afirka suna aiki da harsuna sama da 2,000, amma a yanzu suna rungumar fasahar zamani a ayyukansu.

Yadda na'urorin zamani suke shiga aikin fassara gadan-gadan

Daga Mazhun Idris

"Haba ba Hausa ba ce kawai..."

A'a ba haka zancen yake ba, kamar yadda wani babban banki ya gano a shekarar 2009, bayan ya kashe dala miliyan 10 wajen sake kera kayayyakin da aka rubuta taken kamfanin mai cewa – "Ka dauka babu komai" – wanda aka yi kuskuren fassarawa zuwa "Kar ka yi komai" a kasashen da ba sa magana da Ingilishi.

Haka ma wani kamfanin sayar da soyayyun kaji ya gamu da irin wannan kuskuren lokacin da ya bude reshensa a birnin Beijing na China, inda aka yi kuskuren fassara taken kamfanin zuwa "Cinye yatsunka".

Shekaru 10 bayan nan a Gabashin Tekun China, an samu wani sabani tsakanin wani tsohon tauraron fim dan Amurka, da wata mata, inda batun ya nuna wa duniya yadda "matsalar fassara" a bakuwar kasa zai iya haifar da asara ko rashin sa'a.

Yanzu idan a ce ga wata nahiya da take da harsuna sama da 2,000 cikin kasashe 54: wato Afirka. A zahiri ma, harsunan Afirka suna cikin wadanda suke da karancin kayan aikin yin fassara a duniyar dijital da ta intanet.

A shekarar 2017, Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana kowace ranar 30 ga watan Satumba a matsayin Ranar Fassara ta Duniya, domin tunawa da ayyukan masu fassara, "wadanda suke kokari saukaka rayuwar duniya ta hanyar kawar da tarnakin bambancin harshe".

Mafari

Zuwa karni na 19, lokaci ne da aikin fassara ya zama sahihin fanni na nazari a fadin duniya.

Daga nan kuma an samu gagarumin tasirin kirkire-kirkiren fasaha: da farko, an samu na'urar rediyo a farkon karni na 20, sai kuma aka samun akwatin talabijin bayan ;yan gwamman shekaru.

Bayan wannan kuma sai aka samu yaduwa da karbuwar harsunan duniya wanda ya kawo babban canji, wato bayyanan kwamfutar amfanin mutum guda. Amma za mu tattauna kan wannan daga baya.

A shekarun baya-bayan nan, an sama muhimmin cigaba a fannin intanet da fasahar adana bayanai, aikin fassara ya samu sauyi cikin hanzari, a matsayin fannin nazari da kuma sana'a.

Daga nan fannin na'urorin zamani da suke sarrafa aiki ta dijital, da kwamfuta da intanet, wadda ta karfafa masana'antar fassara.

Gloria Francis, wata mai fassarar Swahili ce kuma edita a mafanin Digital Divide Data da ke Nairobi a Kenya.

Ta fada wa TRT Afrika cewa ta dalilin gamayyar duniya a fannin kasuwanci da tallafin fasaha, aikin masu fassara ya kara samun tagomashi da muhimmanci.

"Baya ga kawar da tarnakin bambancin harshe, masana'antar fassara ta habaka gamewar kasuwannin, ta dalilin fasaha, ta kuma saukaka kashe kudi n yin manyan ayyuka.

Harsunan Afirka za su iya cin moriyar fasahar fassara don samun wakilci mai inganci a sha'anin duniya."

Tallafin fasaha

Shuhurar da kwamfuta ta samu a matsayin na'urar da kowa ke iya saya, wanda ya faro tun a shekarun 1970s, wannan shi ne hakikanin kwararrun fassara da ake bukata don yada bayanai cikin sauri.

Kwamfuta ta zamo abokiyar aiki, inda aka samu sauyi daga ydda aikin yake a baya, inda ake amfani da alkalami, da tawada, da takarda, da tafireta.

Bayan juyin da aka samu daga amfanin da takardar zahiri zuwa ta dijital ya samu kammaluwa ta dalilin kwamfuta kafin daga baya intanet ta zo ta rufe kofar komai.

Karin damarmaki ga masu fassara sun kara samuwa a hankali, sakamakon samu damar yin ayyauka daga masu ba da aiki daga fadin duniya ta dalilin mu'amalar nesa, wanda ya taimaki masu fassarar kananan harsuna.

Mohammad Arabi Umar, wani kwararren mai fassarar Hausa kuma malamin jami'a a sashen nazarin harsuna da al'adu ta Jami'ar Tarayya ta Gusau, da ke Nijeriya.

Ya fada wa TRT Afrika, cewa "Kasa da shekaru 20, ina amfani ne da alkalami da takarda da kamus da rubutaccen jerin kalmomi.

"A yau, duka wadannan suna cikin kwamfutata, ko wayata, har ma da karin abubuwa."

Akwai bukatar a karfafa fasaha don saukaka ayyukan fassara. "Nijeriya tana da harsuna sama da 300, amma tsarin koyar da nazarin fassara a manyan makarantu yawancin ya mayar da hankali kan fikirar fassara da aikin hannu," in ji Umar.

Gloria tana ganin fasaha za ta iya taimakawa masu fassara a Afirka ta hanyar saukaka samar da fassara mai inganci wadda za ta isar da cikakkiyar manufar harsunan Afirka, da habaka ilimi da koyar da harsunan gargajiya.

Bukatar kari

Girman tasirin na'urar kwamfuta a matsayin na'urar da ake siyarwa, ya fara a shekarun 1970s, ya haifar da nasarar samun karbuwar kwamfuta tun daga lokacin nan.

Cikin kankanin lokaci, kwamfuta ta zamo abokiyar aikin masu fassara wadanda ke bukatar yin ayyuka cikin sauri, da fito da bayanai cikin hanzari.

A baya, masu fassara sun yi amfani da alkalami da takarda, sai kuma tafireta tangaraho.

Sauyin daga takarda zuwa kwamfuta ya cika ne ta dalilin karbuwar kwamfuta a ofisoshi da gida, kafin daga bisani intanet ta cike gibin.

Mohammad Arabi Umar, ya ce “Salon fassara a zamanin yau zai iya yin tsauri ga wadanda ba su nakalci kwamfuta ba, wato irin masu fassarar zamanin baya.”

Masamar bayanai ta yanar gizo

Domin kyawu da inganci, masu fassara na bukatar gudanar da bincike sosai a kamus, litattafai, ma'ajiyar bayanai da sauran rubutattun bayanai na hukuma. Yau, nau'in wadannan bayanai na zuwa ta yanar gizo ko manhaja.

Juyin juya halin ya bayar da dmaar samun bayanai cikin sauki da rahusa ta yanar gizo, misali jaridu, kundin encyclopedia, litattafan yanar gizo, hotuna, sauti, bidiyo da sauran kafafan sadarwa.

Masu fassara ba sa bukatar dauka ko bude daruruwan shafuka don samun bayanai. "Tare da isassun masamar bayanai, 'bijimin mai fassara' da yake kiyaye ka'idojin nahawu na wani yare guda, to zainiya fassarar sa a saukeke." in ji Gloriya yayin tattauna wa da TRT Afirka.

Amma Umar na da ra'ayi na daban kan wannan batu. "Duk da dabarun zamani na sauya al'amura, idan ka kalli tsarin koyar da fassarar da muke yi, za ka ga babu amfani da cigaban kwamfuta sosai."

"Kwanan nan. an ba ni aikin samar da daftarin tain koyo da koyarwa na nazarin fassara a matakin karamin digiri.

Amma sai na samu makarantu da dama ba su shigar da fasahar zamani ta amfani da kwamfuta cikin tsarinsu ba." in ji Umar.

Nan ne inda ke bukatar a duba yiwuwar amfani da fasahar zamani ta yadda hakan kuma zai karade ko'ina.

Umar ya yi bayani game da amfani da kwamfuta da ma'ajiyar bayani ta cloude wajen yin fassara kamar su SDL Trados, MemoQ, Xbench, Memsource da Wordfast, wanda suke da kundin fassara kunshe a cikinsu, da kuma taimakon kirkirarriyar fasaha da take gano kura-kurai da rashin daidai, sannan ta auna kyau da ingancin fassara don kyautata dadin karatu.

#