An gudanar da bikin Ranar Afirka a Istanbul tare da baje kolin al'adu, zane-zane, kiɗa da tattaunawar ilimi, inda mahalarta suka tattauna muhimmancin hadin kan nahiyar da musayar al'adu.
Kungiyar Africa Without Borders ta shirya bikin Ranar Afirka a birnin Istanbul tare da halartar ɗalibai, jami'an diflomasiyya, kungiyoyin fararen hula da wakilan kasashen Afirka.
A yayin taron an gabatar da al'adun kasashe daban-daban ta hanyar kiɗa, rawa, fasahar zane da kuma tattaunawa kan makomar nahiyar.
Masu shirya taron sun bayyana cewa irin wadannan shirye-shirye suna kara fahimtar juna tsakanin al'ummomi tare da karfafa dangantakar al'adu tsakanin Afirka da Türkiye.
Maharta sun kuma yi kira ga matasan Afirka su ci gaba da amfani da ilimi da kirkire-kirkire wajen gabatar da kyawawan al'adun nahiyar ga duniya.
