Bidiyon ya nuna an ɗaure hannayensu a bayansu, an rufe musu idanu, kuma an tilasta musu tafiya kan layi suna sunkuyar da kawunansu, yayin da sojojin Isra'ila da 'yan sanda suka kewaye su.

Wani bidiyo ya nuna yadda Isra'ila ke cin zarafin fursunonin Falasɗinawa gabanin sakin su

Wani bidiyo da ya yaɗu ya nuna yadda sojojin Isra'ila suka rinƙa cin zarafin fursunonin Falasɗinawa da aka tara a gidan yarin Negev da ke kudancin Isra'ila, kafin a sako su a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas.

Bidiyon, wanda Ofishin Watsa Labaran Fursunonin Falasɗinu ya wallafa kuma kafofin watsa labarai na Isra'ila suka ambata, ya nuna fursunonin an ɗaure hannayensu a bayansu, an rufe musu idanu, kuma an tilasta musu tafiya kan layi suna sunkuyar da kawunansu, yayin da sojojin Isra'ila da 'yan sanda suka kewaye su.

Ofishin Watsa Labaran Fursunonin ya bayyana cewa bidiyon "yana nuna wani yanayi mai raɗaɗi da ke bayyana yadda aka ci zarafin fursunonin da za a sako su ƙarƙashin yarjejeniyar musayar fursunoni."

Amjad al-Najjar, shugaban Ƙungiyar Fursunonin Falasdinu, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa "kafofin watsa labarai na Isra'ila sun wallafa wani bidiyo daga gidan yarin Desert da ke nuna shirye-shiryen sakin wasu fursunonin Falasɗinu."

Ya ce fassarar bidiyon ta nuna cewa waɗanda aka nuna a ciki su ne fursunonin da ke da hukuncin ɗaurin rai da rai, wadanda aka tura zuwa gidan yarin Negev kafin a kora su zuwa Gaza a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar.

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Shaidu sun bayyana wa Anadolu cewa sojojin Isra'ila sun kai farmaki gidajen wasu fursunoni a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, suna gargaɗin iyalai kada su gudanar da bukukuwan murnar sakin 'yan uwansu.

Daga cikin gidajen da aka kai farmaki akwai na Khalil Abu Aram, Taleb Makhmara da Murad Id’ees, waɗanda suna daga cikin waɗanda za a sako.

A baya, wasu fursunonin Falasɗinu sun kira iyalansu don bayyana farin cikinsu kan tsammanin sakin su a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Al-Quds ta ruwaito.

Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Isra'ila ta tabbatar da cewa dukkan fursunonin da aka tsara za a sako an tura su zuwa wuraren da za a sako su.

Karkashin matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, za a sako fursunonin Falasdinu 2,000 — ciki har da 250 da ke da hukuncin ɗaurin rai da rai da kuma 1,700 da aka tsare tun watan Oktoba 2023 — a musayar su da mutum 48 da aka yi garkuwa da su na Isra'ila.

Ma’aikatar Shari’a ta Isra’ila ta wallafa sunayen fursunoni 250 a ranar Jumma’a.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#