An miƙa rukuni na biyu na fursunonin Isra'ila 13 ga ƙungiyar Red Cross, bayan sakin guda bakwai na farko a ranar Litinin.

Hamas ta kammala sakin 'yan Isra'ila 20 da ta tsare a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta

Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu, Hamas ta miƙa ƙarin fiye da ‘yan Israila 13 da take tsare da su a Gaza zuwa ga Ƙungiyar Jin-ƙai ta Red Cross, cewar gidajen labarai a Isra’ila.

Rahotannin Channel 12 sun ce ranar Litinin ICRC ta karɓi fursunonin Isra’ila 13 daga reshen mayaƙan Hamas, Qassam Brigades, kuma a yanzu suna kan hanyarsu ta zuwa Isra’ila.

Bayan miƙa fursunonin 13, an kammala sakin duka ‘yan Isra’ila 20 da ke raye, ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan an saki rukunin farko na mutum bakwai tun da fari a ranar Litinin.

An yi musayar tsararrun ‘yan Isra’ilan ne da fursunonin Falasɗinu 1,968, ciki har da 250 da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai, waɗanda za a saka ƙarƙashin yarjejeniyar ta Gaza.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#