Dollar

41,4779

0.08 %

Euro

48,8450

0.3 %

Gram Gold

4.986,8000

0.16 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugabannin Ƙasashen Musulmai sun matsa wa Trump lamba kan ya yi gaggawar goyon bayan samar da tsagaita wuta a Gaza, da shigar da tallafi da samar da tsarin 'yancin kan Falasɗinu, suna gargadin samun tashin hankali a yankin in aka ci gaba da yaƙin.

UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan

Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar wa shugabannin Musulmi cewa ba zai bari Isra'ila ta ƙwace yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ba, kamar yadda jaridar Politico ta ruwaito a ranar Laraba, tana ambaton mutane shida da suka san batun.

Trump ya yi wannan alkawari ne a yayin wani taro na sirri da aka gudanar a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, inda shugabannin Larabawa da Musulmi suka matsa wa Washington lamba kan ta mayar da hankali wajen kawo karshen yakin Isra'ila a Gaza.

A cewar jaridar Politico, ma’aikatan Trump sun rarraba wata takarda mai bayyana shirin gwamnatinsa na dakatar da rikicin, wanda ya hada da alkawarin hana mamaye yankin.

Taron, wanda aka shirya tare da goyon bayan Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya hada shugabannin kasashe kamar na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Sarkin Jordan Abdullah II, Shugaban Indonesia Prabowo Subianto, Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, Firaministan Masar Mostafa Madbouly, Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, da Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan.

‘Samar da zaman lafiya mai ɗorewa da adalci’

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da Riyadh ta fitar, shugabannin sun bayyana cewa kawo karshen yakin Gaza shi ne “mataki na farko wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa da adalci.”

Sun gargadi duniya kan “mummunan bala’in jinƙai” da kuma yawan mutanen farar hula da suka rasa rayukansu, inda hukumomin lafiya na Gaza suka ruwaito cewa sama da Falasdinawa 65,000 ne suka mutu tun watan Oktoban 2023.

Sun yi watsi da duk wani yunkuri na tilasta wa Falasdinawa barin gidajensu, tare da bukatar tsagaita wuta nan take wanda zai ba da damar dawowar wadanda aka raba da gidajensu, da kuma isar da tallafin jinƙai ba tare da wani cikas ba.

Haka kuma, sun bukaci samar da wata hanya ta tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Yammacin Kogin Jordan da wuraren ibada masu tsarki na Birnin Kudus da gyare-gyare a cikin Hukumar Falasdinawa, da kuma wani shirin sake gina Gaza gaba daya karkashin jagorancin Larabawa da Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi, OIC.

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya kwanan nan sun kammala cewa Isra'ila tana aikata kisan kare dangi a Gaza, inda yawancin yankin ke fuskantar yunwa da bala’i da aka haddasa bayan shekaru na hare-hare.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#