Dollar

41,3033

0.05 %

Euro

48,8714

0.14 %

Gram Gold

4.870,8300

0.28 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rahotanni sun ce Netanyahu ya shaida wa Trump cewa ya samu wata ‘yar ƙaramar dama ce ta kai wa Qatar hari inda ya yi amfani da damar.

Trump ya yi tattaunawa mai zafi da Netanyahu kan harin Isra'ila a Qatar – Rahotanni

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wata tattaunawa mai zafi ta waya da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda ya bayyana "babban takaicinsa" kan yadda aka shammace shi game da harin da Isra'ila ta kai kan wakilan Hamas a Qatar, kamar yadda jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito.

A wani rahoto na musamman da aka wallafa a ranar Laraba, Manyan jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa Trump ya shaida wa Netanyahu cewa matakin da ya ɗauka kan kai hari kan shugabannin siyasa na kungiyar Falasdinawa a Doha, babban birnin Qatar, babu hikima a ciki. Ya kuma bayyana cewa "ya fusata sosai da jin labarin harin daga sojojin Amurka—maimakon daga Isra'ila—kuma hakan ya faru a yankin wata abokiyar ƙawancen Amurka wanda ke shiga tsakani don kawo karshen yakin Gaza."

Netanyahu ya shaida wa Trump cewa ya samu wata ‘yar ƙaramar dama ce ta kai wa Qatar hari inda ya yi amfani da damar.

Bayan wannan tattaunawar, an sake kiran waya na biyu a tsakaninsu inda aka yi wayar a cikin lumana, inda Trump ya tambayi Netanyahu ko harin ya yi nasara. Netanyahu bai iya bayar da tabbacin nasarar ba.

Daga baya, Hamas ta tabbatar cewa shugabanninta sun tsira daga harin, yayin da mambobi biyar na kungiyar da wani jami'in tsaro na Qatar suka rasa rayukansu.

Trump ya fusata da Netanyahu

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#