Sport
Dollar
41,3098
0.07 %Euro
49,0047
0.41 %Gram Gold
4.871,8300
0.3 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi.
Mutane 19 sun mutu a jihar kudancin India ta Kerala a 2025 sakamakon kamuwa da cutar ‘amoebic meningoencephalitis’ (PAM) mai cinye ƙwaƙwalwa, in ji Kwamishinar Lafiya ta jihar Veena George.
George ta ce jimillar mutane 69 ne suka kamu da cutar a wannan shekarar.
Jihar ta bayar da sanarwar kar ta kwana a yayin da cutar ke yaduwa, tashar talabijin din jihar DD ta rawaito hakan.
Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi, in ji Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka CDC.
Ana yawan kiran cutar da ‘Amoeba mai cinye kwakwalwa” saboda tana iya kama kwakwalwar tare da lalata jijiyoyi da fatar ƙwaƙwalwar, kamar yadda aka bayyana a shafin intanet na CDC.
Comments
No comments Yet
Comment