Dollar

42,2403

0.06 %

Euro

48,7670

-0.24 %

Gram Gold

5.562,7400

2.37 %

Quarter Gold

9.385,1300

1.77 %

Silver

68,2200

3.8 %

Shugaban Turkiyya da shugabannin siyasa da manyan jami’an shari’a da jami’an soji da sauran wakilan ƙasa sun taru a Anitkabir a birnin Ankara domin karrama Mustafa Kemal Ataturk, da ya assasa ƙasar kuma shugabanta na farko.

Turkiyya na jimamin tunawa da rasuwar Ataturk shekara 87 da suka wuce

Mustafa Kemal Ataturk, wanda ya assasa jamhuriyyar Turkiyya, ana jimamin tunawa da shi ranar Litinin bayan ya shekara 87 da rasuwa inda aka yi wani biki na ƙasa a hukumance a Anitkabir, inda kabarinsa yake a babban birnin ƙasar Ankara.

An fara bikin ne wanda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya halarta tare da shugaban majalisar dokoki Numan Kurtulmus, da ‘yan majalisar ministoci da shugabannin jam’iyyar siyasa da manyan jami’an fannin shari’a da kwamandodin soji.

Erdogan ya ajiye fure mai launin fari da ja da aka sarrafa kamar tutar Turkiyya kan kabarin Ataturk.

Da misalin ƙarfe 9.05 na safiya (ƙarfe 06:05 agogon GMT), lokacin da Ataturk ya rasu, waɗanda suka halarci taunawar sun yi shiru na wani lokaci, kuma bayan haka suka rera waƙar ƙasar. A lokacin yabo, an yi ƙasa-ƙasa da tutar Turkiyya.

Daga bisani, Erdogan da jami’an da suka raka shi sun nufi Benen Misak-i Milli, inda ya saka hannu a Littafin Tunawa na Anitkabir, inda ya yaba wa Ataturk da abokan gwagwarmayarsa.

"Muna tsananin kare Jamhuriyar Turkiyya, wanda ka kira ‘aikinka mai girma,’ kuma mun ci gaba da ƙawata ko wane inci na ƙasarmu da sabbin nasarori," kamar yadda Erdogan ya rubuta.

"A ƙarƙashin shugabancin ƙwararrun mutane, Turkiyya tana ci gaba da taku na aminci a kan hanyarta ta zama ƙasa mai ƙarfi a duniya," a cewarsa.

Ataturk ya kasance shugaban ƙasar na farko har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba na shekarar 1938, lokacin da ya rasu yana mai shekara 57 sakamakon wata cuta ta hanta da ake ce wa cirrhosis a Ingilishi.

Mutanen Turkiyya suna da al’adar zuwa kabarinsa a duk ranar 10 ga watan Nuwamba domin girmama wanda ya assasa ƙasar.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#