Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Yayin da yake jawabi a wani biki na tunawa da cikar shekaru biyar da nasarar Azerbaijan a Karabakh, Erdogan ya yaba game da kawo ƙarshen mamayar da ta ɗauki tsawon shekaru 30 ta Armenia.
Turkiyya ta jaddada goyon bayanta da kiran samar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin Azerbaijan da Armeniya yayin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya gabatar da saƙo a Baku a ranar Asabar.
Yayin da yake jawabi a wani biki na tunawa da cikar shekaru biyar da nasarar Azerbaijan a Karabakh, Erdogan ya yaba game da kawo ƙarshen mamayar da ta ɗauki tsawon shekaru 30 ta Armeniya, yana bayyana hakan a matsayin wata shekara mai juyin-juya hali ga yankin Caucasus.
Ya ce 'yantarwar ba wai ta dawo da adalci kadai ba ce, har ma ta buɗe sabon zamani na zaman lafiya da daidaito a yankin, yana ƙarfafa kowa da kowa da su mayar da nasara zuwa zaman lafiya mai ɗorewa.
“Ba ma riƙe abu a ranmu, sannan ba za mu manta da ciwon da muka ji a baya ba. Bai ka mata wannan zaman lafiyar ya zama ƙarshe kawai ba,” in ji Erdogan, inda ya kira lamuran da suka faru bayan yaƙin a matsayin lokaci na sulhu.”
Ƙarfafa haɗin gwiwa
Shugaban kasar Turkiyya ya yaba wa Shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan saboda kokarin da yake yi wajen neman cim ma yarjejeniyar zaman lafiya da Armeniya, da kuma amincewa da matakan da suka kamata waɗanda Firaiministan Armeniya Nikol Pashinyan ya ɗauka.
Wadannan matakai ne na jarumta da kyakkyawar manufa daga shugabanni biyu; muna da yakinin cewa wata yarjejeniya mai ɗorewa za ta kammala wannan tsari, wadda za ta tabbatar da zaman lafiya a yankin, kamar yadda Erdogan ya ce, inda ya ƙara da cewa Turkiyya a shirye take ta tallafawa wannan tsari ta kowace hanya.
Erdogan ya kuma nuna girmamawa sosai ga sojojin Azerbaijan da tsofaffin sojojinsu da suka yi yaƙi a Karabakh, inda ya bayyana gwagwarmayarsu a matsayin jarumtaka.
Yayin da yake jaddada ƙaruwar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, Erdogan ya bayyana cewa manyan ayyukan makamashi kamar bututun iskar gas da hanyoyin sufuri na ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen.
Comments
No comments Yet
Comment