Dollar

42,2373

0.06 %

Euro

48,7932

-0.18 %

Gram Gold

5.544,4700

2.03 %

Quarter Gold

9.385,1300

1.77 %

Silver

67,7400

3.07 %

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin arewacin Nijeriya wadanda ake da zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan aka kwatanta da sauran yankin da matsalar tsaro ta yi kamari.

Damuwa kan kutsawar 'yan bindiga Jihar Kano

Ana ci gaba da nuna fargaba da kuma damuwa dangane da yadda ake ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe da sace-sacen mutane don neman kudin fansa da kuma aikace-aikacen ’yan bindiga a wasu sassan Jihar Kano.

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin arewacin Nijeriya wadanda ake da zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan aka kwatanta da sauran yankin da matsalar tsaro ta yi kamari.

Jihohin arewacin kasar kamar Zamfara da Kaduna da Katsina su ne matsalar tsaro ta fi kamari kuma masana harkokin tsaro suna ganin cewa kasancewar Jihar Kano ta yi makwabtaka da jihohin Katsina da Kaduna hakan ne ya jefa ta cikin barazanar kwararar ’yan bindigar da suka addabi makwabtan nata.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa matsalar tsaron da ake gani yanzu ta ’yan bindiga tana faruwa ne a wasu kauyuka da ke Kananan Hukumomin Tsanyawa da kuma Shanono, wadanda suke da iyaka da Jihar Katsina.

SP Kiyawa ya ce jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen dakile wannan babbar barazana, sannan zuwa yanzu sun kama wasu mutum uku wadanda ake zargi, kuma suna fadada bincike a kansu.

Ya ce rundunar ’yan sanda sun yi nasarar kama mutanen da ake zargin ’yan bindiga ne masu satar mutane domin kudin fansa a karshen watan jiya, bayan samun wasu bayanan sirri.

Sannan idan za a tuna a makon jiya ne rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kashe wasu ’yan bindiga 19 a jihar, yayin wani artabu da dakarunta suka yi da su a Jihar Kano kuma sakamakon haka sojoji biyu sun mutu da wani dan sa-kai guda daya, kamar yadda mai magana da yawun rundunar Babatunde Zubairu ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Sojojin sun kai farmaki ne wata maboyar ’yan bindigar a Karamar Hukumar Shanono tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaron kasar.

Kazalika Shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya kuma masani kan al’amuran da suka shafi tsaro Dokta Kabiru Adamu ya ce dalilai da dama ne suka jawo bullar matsalar tsaro Jihar Kano, ciki har da wasu matakai da wasu jihohi makwabtanta suke dauka kamar matakin sulhu da aka yi da su a Jihar Katsina.

Masanin ya ce wajibi ne hukumomi su tashi tsaye wajen yaki da wannan matsala saboda yadda matsalar take gurgunta rayuwar al’umma gaba daya, kuma ya ce Jihar Kano jiha ce mai muhimmancin gaske ga arewacin Nijeriya, wanda ya ce idan wannan matsala ta mamaye ta, to matsalar za ta iya shafar gaba daya arewa.

Dokta Kabiru Adamu ya ce duk da cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen magance matsalar, akwai bukatar ta samar da wani tsarin musamman na matakan tsaro irin wanda ake da shi a wasu jihohin kasar kamar Jihar Legas.

Ya ce saboda girman Jihar Kano da kuma muhimmancinta, kamata ya yi gwamnan Kano ya kafa matakan tabbatar da tsaro a matakin al’ummomi cikinsu har da samar da hanyar gano matsalar tsaro da wuri tun kafin abin ya zama babbar matsala.

Ya ce tsarin zai hada da samar da wasu lambobin gaggawa da kowane mazaunin Kano idan yana cikin matsala zai iya kiran jami’an tsaro a ko yaushe, kuma jami’an tsaron su kai masa dauki a cikin mintuna bakwai zuwa 15 a ko ina yake a cikin jihar. Ya ce ta haka ne za a iya dakile wannan matsala tun daga tushe.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#