Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Charles Chukwuma Soludu ya samu nasarar samun wa'adi na biyu bayan ya samu ƙuri’u 422,664, yayin da Nicholas Ukachukwu na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya biyo baya da ƙuri’u 99,445.

INEC ta ayyana Charles Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Anambra

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Charles Chukwuma Soludo na Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya.

Farfesa Edoma Omoregie, wanda shi ne babban bautren zaɓe na jihar ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon ta INEC da ke Awka, babban birnin jihar, da safiyar Lahadi.

A cewar sakamakon, Soludo ya samu ƙuri’u 422,664, yayin da Nicholas Ukachukwu na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya biyo baya da ƙuri’u 99,445.

Paul Chukwuma na Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ne ya zo na uku a zaɓen da ƙuri’u 37,753.

George Moghalu na Jam’iyyar Labour Party (LP) ne ya zo na huɗu da ƙuri’u 10,576, yayin da Jude Ezenwafor na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu ƙuri’u 1,401.

Wannan sakamakon ya bai wa Soludo sabon wa’adin shekaru huɗu a gidan gwamnati na Light House da ke Awka.

Jam’iyyu goma sha shida da ‘yan takararsu ne suka fafata a zaɓen kujerar gwamnan Anambra.

Baya ga Soludo da Ukachukwu, sauran sun haɗa da John Nwosu na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Charles Soludo dai ya kasance tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN daga 2004 zuwa 2009 sannan ya zama gwamnan Anambra a shekarar 2022.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#