Dollar

38,6815

-0.24 %

Euro

43,4935

0.27 %

Gram Gold

3.972,8500

0.3 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ministan Harkokin Wajen Hakan Fidan ya bayyana irin rawa mai muhimmanci da Turkiyya ke takawa yayin da ministan harkokin wajen NATO suka yi taro a Antalya a lokacin da ake ƙoƙarin yin sulhu a rikicin Ukraine.

Turkiyya na fatan tattaunawar Istanbul za ta buɗe sabon shafin sulhu tsakanin Ukraine da Rasha

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana fatan cewa tattaunawar zaman lafiya da za a yi tsakanin Ukraine da Rasha a Istanbul ranar Alhamis za ta iya zama wata hanya ta sabon mafari tsakanin ɓangarorin biyu da ke rikici.

“Yanzu, bayan shekaru uku ana shan wahala mai tsanani, akwai damar da za a iya amfani da ita,” in ji Hakan Fidan a jawabinsa na maraba yayin buɗe taron ministocin harkokin wajen NATO.

Ana sa ran Rasha da Ukraine za su gudanar da tattaunawar zaman lafiya kai tsaye a Istanbul — karo na farko cikin kusan shekaru biyu — tare da Turkiyya tana sake zama mai masauki da mai shiga tsakani.

“Tattaunawar a Istanbul, in Allah ya yarda, za ta iya buɗe sabon babi,” in ji Fidan.

Fidan ya kuma jaddada buƙatar kafa tsarin tsaro mai ƙarfi a faɗin ƙasashen NATO daga jihar Texas ta Amurka zuwa babban birnin Turkiyya, Ankara.

Da yake magana da manema labarai a rana ta biyu ta taron ministocin NATO, Fidan ya jaddada muhimman abubuwan da ke faruwa a yankin Turai da Atalantika.

“A matsayinmu na abokan ƙawance, yau za mu yi muhimman tattaunawa daga yadda za a raba nauyin tsaron, da yadda za a ƙarfafa masana'antar tsaronmu, da yadda za a kawo zaman lafiya ga Ukraine.”

Ya ce abokan ƙawancen za su mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da kuma ci gaba da ƙoƙarin cim ma zaman lafiya a Ukraine.

Fidan ya ƙara da cewa taron zai kuma zama matakin shirye-shiryen taron ƙolin NATO da za a gudanar a watan Yuni a birnin Hague.

Da abubuwan da suke faruwa na diflomasiyya a Antalya da Istanbul a lokaci guda, Turkiyya tana tabbatar da kanta ba kawai a matsayin babbar ƙawar NATO ba, har ma a matsayin cibiyar diflomasiyya mai tasiri wajen warware rikice-rikicen ƙasa da ƙasa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#