Dollar

41,0041

0.14 %

Euro

48,0993

0.95 %

Gram Gold

4.442,7600

1.09 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Hukumomi a Turkiyya za su binciki Google kan tilasta wa manhajoji amfani da tsarinsa na biyan kuɗi da kuma hana mutane amfani da wasu hanyoyin biyan kuɗi na daban.

Turkiyya na binciken Google kan tilasta wa manhajoji amfani da tsarin biyan kuɗi na Play Store kaɗai

Turkiyya ta ƙaddamar da bincike kan kamfanin Google saboda yadda yake sanyawa ana biyan kuɗi a manhajar Play Store, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan gasa ta bayyana ranar Juma’a.

"An fara bincike game da GOOGLE domin gane ko GOOGLE ya saɓa wa doka ta 4054 kan Kare Gasa (doka mai lamba 4054) in ji sashe na 41 na dokar," kamar yadda Hukumar da ke saido kan gasa ta Turkiyya ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Binciken zai mayar da hankali ne kan zargin cewa Google ya saɓa wa dokokin gasa ta hanyar neman masu haɗa manhajoji da ke son su tallata manhajojinsu kan manhajar Play Store ta Google su yi amfani da tsarin biyan kuɗinsa, Google Play Billing (GPB), da kuma hana masu haɗa manhajoji bayyana wa masu amfani da manhajojinsu wasu tsare-tsaren biyan kuɗi da za su iya amfani da su a madadin na Google ɗin.

An gudanar da wani  bincike na share fage a matsayin wani ɓangare na “nazari kan yanayin yadda harkar amfani wayar salula”, lamarin da ya ƙara zaton cewa Google na ƙaƙaba taƙaita amfani da tsare-tsaren biyan masu haɗa manhajoji.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#