Sport
Dollar
41,1434
0.12 %Euro
48,3350
0.95 %Gram Gold
4.432,1000
0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Saƙon farko da Erdogan ya wallafa ya zo ne a yayin da sabon dandalin na Turkiyya ‘NEXT Sosyal,' ya samu mutane fiye da miliyan ɗaya da ke amfani da shi kana ya samu matsayi na gaba-gaba a jerin jadawalin manhajoji da ake da su na wayar hannu.
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya wallafa saƙonsa na farko a shafinsa na NEXT Sosyal, wani sabon dandalin sada zumunta na ƙasar da ke bunƙasa cikin sauri.
Shugaban ya wallafa wani baiti daga cikin waƙar Erdem Bayazit ‘‘Soon the Day Will Rise - "A flower sprouted between concrete walls’’ wato “Ba da daɗewa ba Rana Za Ta Fito- "Fure zai yi yaɗu a tsakanin bangon kankare" - a ranar Litinin Erdogan ya tambayi mabiya daga dandalin, "Shin kun shirya?"
Bayan saƙon nasa, ya yi mafani da maudi’i “We’re starting” (mun fara) da kuma alamar tutar ƙasar Turkiyya da Duniya da kuma kumbo.
Me nene Next Sosyal?
Sakon da shugaban ya wallafa na zuwa ne a yayin da dandalin Next Sosyal, wanda aka ƙirƙire shi ƙarkashin jagorancin ‘Turkiye Technology Team (T3) Foundation’ wato tawagar gidauniyar fasaha ta Turkiyya (T3) ya samu mutane fiye da miliyan ɗaya da suke amfani shi.
Comments
No comments Yet
Comment