Dollar

41,1434

0.12 %

Euro

48,3350

0.95 %

Gram Gold

4.432,1000

0.84 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Turkiyya na goyon bayan kokarin sulhu a Libya da ke da manufar dabbaka hadin kai da ‘yaacin mulkin kasar.

Turkiyya na ƙara ƙoƙarin ganin an samar da Libya 'mai haɗin kai kuma dunƙulalliya'

Turkiyya na hanzarta gudanar da ayyukan diflomasiyya don kawo karshen rikicin cikin gida a Libya tare da samar da “Libya mai hadin kai kuma dunkulalliya” kamar yadda majiyoyin Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya suka bayyana.

Kokarin ya faro ne tare da ziyarar da Kwamandan Sojojin Kasa na Libya Lutanal Janar Saddam Haftar ya kai Turkiyya a watan Afrilun 2025.

A farkon makon nan, jirgin ruwan sojin Turkiyya na TCG Kinaliada ya ziyarci tashar jiragen ruwan Tarabulus inda ya jagoranci tattaunawa tsakanin Jakadan Turkiyya a Libya, Guven Begec, da Ministan Tsaro na Libya, Shugaban Rundunar Soji, Kwamandan Sojojin Ruwa, Kwamandan Dakaurn Tsaron Iyakokin Teku da Kwamandan da ke Tarabulus.

Ana sa ran TCG Kinaliada zai ziyarci tashar jiragen ruwa ta Benghazi ranar Larabar nan, inda za a yi karamin bikin tarbar baki na soji da ziyara a hukumance.

Mataki mai dauke da dabarun zaman lafiya

Wannan ziyarar na nuni da tsarin da Turkiyya ke da shi na hada kai da samar da kwanciyar hankali ga daukacin kasar Libya, da kuma wata sabuwar alama d ake bayyana manufofinta na rungumar daukacin kasar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#