Sun ce ayyana yankuna a matsayin “filin ƙasa” ya karya dokokin ƙasa da ƙasa

Kasashe Takwas Sun Yi Allah Wadai Da Matakin Isra’ila A Gaɓar Yamma

Ministocin harkokin wajen Turkiyya, Masar, Jordan, Indonesia, Pakistan, Qatar, Saudi Arabia da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa a ranar Talata suna Allah wadai da matakin Isra’ila na ayyana manyan yankuna a Gaɓar Yamma da aka mamaye a matsayin “filin ƙasa”, suna mai kiran matakin babban wuce-gona-da-iri.
TRT Hausa

A cewar sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar, ministocin sun soki amincewar Isra’ila da shirin yin rijista da daidaita mallakar filaye a yankuna da dama na Gaɓar Yamma da aka mamaye, suna cewa matakin haramun ne kuma zai hanzarta faɗaɗa matsugunan ‘yan kama wuri zauna da ƙwace filayen Falasɗinawa.
TRT Hausa

Ministocin sun bayyana cewa matakin ya saba wa dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, ciki har da Yarjejeniyar Geneva ta Huɗu, da kuma ƙudurorin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman Ƙuduri na 2334 wanda ke buƙatar Isra’ila ta dakatar da faɗaɗa matsugunai.
TRT Hausa

Sanarwar ta kuma yi nuni da ra’ayin Kotun Duniya (ICJ), inda ta ce duk wasu matakai da ke sauya matsayin shari’a, tarihi da na al’umma na yankunan Falasɗinu da aka mamaye haramtattu ne a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
TRT Hausa

Ministocin sun yi gargaɗin cewa matakin Isra’ila na iya kawo sabon tsarin shari’a da gudanarwa wanda ke barazana ga mafitar ƙasashe biyu, tare da ƙara tayar da hankula a yankin. Sun kuma yi kira ga al’ummar duniya da su ɗauki matakai masu ƙarfi don kare haƙƙin Falasɗinu da tabbatar da kafa ƙasa mai ‘yanci a kan iyakokin 4 ga Yunin 1967 tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta.
TRT Hausa

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#