An miƙa akwatuna ɗauke da ƙoƙon kawuna da gawarwakin Falasɗinawa zuwa Asibitin Al-Shifa

Corbyn Ya Bayyana Rahoton Gawarwaki Masu Tayarda Hankali Daga Gaza

Dan majalisa mai zaman kansa kuma tsohon shugaban jam’iyyar Labour, Jeremy Corbyn, ya bayyana wani rahoto mai sosa rai daga daraktan Asibitin Al‑Shifa da ke Gaza, inda aka bayyana miƙa akwatuna da dama ɗauke da gawarwakin Falasɗinawa da aka guntule sassan jikinsu.

Corbyn ya ce ya samu saƙo daga Dakta Mohammed Abu Salmiya, wanda ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun miƙa akwatuna 66 na gawarwaki zuwa asibitin. A cewarsa, ma’aikatan asibiti sun buɗe akwatunan inda suka tarar da ƙoƙon kawuna da ƙasusuwa, tare da gawarwakin da ba a iya tantance ko su waye ba.

Rahoton ya ce wasu daga cikin gawarwakin, ciki har da na mata, sun nuna alamun an guntule wasu sassan jikinsu, lamarin da ya haifar da zargin cire sassan jiki. Corbyn ya bayyana abin a matsayin “mai wuya a siffanta,” yana cewa hakan na nuna irin halin da Falasɗinawa ke ciki a halin yanzu.

Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta tabbatar da karɓar gawarwakin ta hannun Red Cross (ICRC), tana mai cewa wasu gawarwakin sun nuna alamun da ba a saba gani ba, ciki har da tsagu na asibiti da ke nuni da yiwuwar an yi musu wasu ayyuka kafin a dawo da su.

Dakta Abu Salmiya ya ƙara da cewa yawancin gawarwakin ba za a iya gane su ba saboda yanayinsu, inda wasu suka ƙunshi ƙoƙon kawuna da ƙasusuwa kaɗai, abin da ya ƙara tayar da hankalin jami’an lafiya a yankin.

Tushen labari: TRT Hausa

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#