Sport
Za a tattauna faɗaɗa matsugunan Isra’ila da yunƙurin haɗa yankunan Falasdinawa
Kungiyar Kungiyar Haɗin Kan Musulmi (OIC) ta sanar da shirinta na gudanar da taron gaggawa na ministocin harkokin wajen ƙasashe mambobinta a ranar Alhamis, domin tattauna matakan Isra'ila na faɗaɗa matsugunan ‘yan kama-wuri-zauna da yunƙurin haɗa yankin da aka mamaye na Yammacin Kogin Jordan cikin ƙasar.
Za a yi taron ne a Jeddah bisa buƙatar Falasdinu, don daidaita matsaya da tattauna hanyoyin ɗaukar mataki kan matakan da OIC ta ce na iya sauya matsayin doka, siyasa da tsarin al’umma na yankin Falasdinu, tare da kawo cikas ga tsarin kafa ƙasashe biyu.
A ranar 15 ga Fabrairu, gwamnatin Isra’ila ta amince da rajistar manyan yankuna a Gabar Yamma a matsayin “mallakin ƙasa,” matakin da aka ce shi ne na farko tun bayan mamayar yankin a 1967.
Kafafen yaɗa labarai na Isra’ila sun ce matakin ya haɗa da buɗe rajistar filaye da aka dade ana dakatarwa, soke dokokin da suka haramta sayar da ƙasa ga Yahudawa, da kuma fitar da bayanan rajista da aka ɓoye tsawon shekaru.
Falasdinawa sun gargadi cewa wannan na iya zama shirin cikakkiyar mamaya, lamarin da zai kawo ƙarshen yiwuwar kafa ƙasar Falasdinu mai zaman kanta bisa ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
Tushen labari: TRT Hausa
Comments
No comments Yet
Comment