Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya buƙaci ’yan majalisar dokokin ƙasar da su rage yawan kuɗaɗen da aka ware don kashe wa a kasafin kuɗi na shekarar 2026, daga naira tiriliyan 68.3 da majalisar ta amince da su a farkon bana zuwa naira tiriliyan 65.2.
A cikin wata wasiƙa da ya aikewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani a ranar Talata, Tinubu ya ce sauye-sauyen da aka gabatar a cikin kasafin kuɗin sun yi daidai da nauyin da gwamnati ta riga ta ɗauka da kuma albarkatun kuɗin da take da su.
Sauye-sauyen da aka gabatar za su kuma taimaka wajen daidaita wasu kuɗaɗen da kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC ya kashe a madadin gwamnatin tarayya, tare da magance matsalolin biyan basussuka waɗanda ba a ware musu isassun kuɗaɗe ba a cikin kasafin kuɗin farko.
Duk da shawarar rage yawan kuɗaɗen da za a kashe gaba ɗaya, gibin kasafin kuɗin gwamnati zai ci gaba da kasancewa a matakin kashi 5.64 cikin 100 na jimillar ƙimar tattalin arzikin ƙasar (GDP), a cewar wasiƙar.
Ana sa ran Ministan Kuɗin Najeriya zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027 ga ’yan majalisa a wata mai zuwa, gabanin babban zaɓen ƙasar da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairu.
Wannan shawarar yin garambawul ga kasafin kuɗin ta zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin daidaita yadda take kashe kuɗaɗen gwamnati da nauyin kuɗaɗen da ta ɗauka da kuma albarkatun kuɗin da take da su.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: AP (Wire)
