Sport
Umarnin na Shugaba Tinubu ya biyo bayan kashe-kashen da 'yanta'adda suka yi ne a wasu ƙauyuka a jihar ta Kwara.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umanin tura wata bataliya ta soji ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara inda ’yan ta’adda suka kashe mutum fiye da 160 a ƙauyen Worro.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce sabuwar rundunar sojin za ta yi aiki ne ƙarƙashin dakaru na musamman na Operation Savannah Shield domin daƙile aika-aikar ‘yanta’adda da kuma kare al’ummomin da ba su da kariya.
Shugaba Tinubu “ya yi Allah wadai da harin na ragwanci da dabbanci kuma ya bayyana ‘yanbindigar a matsayin marasa tausayi da suka zaɓi ƙaddamar da hari na ta’addanci kan wuraren da ke da sauƙin kai hari,” in ji sanarwar.
Shugaba Tinubu ya bayyana ɓacin ransa game da yadda maharan suka kashe mazauna garin waɗanda suka yi watsi da ƙoƙarinsu na “cusa musu aƙidarsu mai muni,” inda suka zaɓi su bi addinin Musuluncin da ba shi da tsauri ko tashin hankali.
"Abin yabawa ne cewa mutanen garin, duk da cewa Musulmai ne, sun ƙi amincewa a shigar da su wata aƙida da ba su saba da ita ba da ta fifita tashin hankali fiye da zaman lafiya da tattaunawa," in ji shi.
Shugaban ya yi kira da a haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi domin ba da taimako ga mutanen garin da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata aika-aikar sun gurbi abin da suka shuka.
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da ta’aziyya ga waɗanda suka rasa ‘yan’uwansu da kuma gwamnatin jihar Kwara.
An kashe fiye da mutum 160
Rahotanni a Nijeriya dai sun ce an kashe sama da mutum 160 da daren Talata bayan wasu masu iƙirarin jihadi sun kai hari ƙauyukan Woro da Nuku a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya tabbatar da kashe mutum 75 .
Gwamnan ya bayyana wannan adadin ne da ranar Laraba da maraice yayin da ya ziyarci fadar sarkin Kaiama, yana mai bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su “Musulmai ne da aka yi wa kisan ƙare-dangi domin sun ƙi miƙa wuya ga masu tsattsaruan ra’ayi da ke tallata wata sabuwar aƙida.”
Rahotanni dai sun ce ana ganin maharan sun fito ne daga gandun dajin Kainji da ke jihar Neja mai maƙwataka.
Jihar Kwara dai tana cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yanta’adda a Nijeriya inda kwanakin baya ‘yanta’adda suka yi awon-gaba da masu ibada a coci a lokacin da ake nuna ibadan kai-tsaye a shafin Facebook.
Comments
No comments Yet
Comment