Red Cross ta ce harin na daga cikin mafi muni da aka gani a Nijeriya cikin ‘yan watanni

An kashe fiye da mutum 160 a mummunan harin ‘yan bindiga a jihar Kwara

Ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta Duniya (ICRC) ta bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe aƙalla mutane 162 a wani mummunan hari da aka kai a daren Talata a wani ƙauye da ke yammacin jihar Kwara, wanda ya zama ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi muni a Nijeriya a baya-bayan nan. TRT Hausa

Harin ya faru ne jim kaɗan bayan da sojojin Nijeriya suka gudanar da wani samame a yankin domin kawar da ‘yan ta’adda. ‘Yan sanda da gwamnatin jihar Kwara sun tabbatar da aukuwar harin, inda suka ɗora laifin kisan kan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda. TRT Hausa

ICRC ta ce adadin waɗanda suka mutu ya karu daga 67 zuwa 162 yayin da ake ci gaba da gano gawawwaki, inda wasu majiyoyi suka ce mutane da dama sun tsere zuwa daji yayin harin da aka kai ƙauyen Woro, tare da ƙona shaguna da fadar sarki. TRT Hausa

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana maharan a matsayin ‘yan ta’adda matsorata. A halin da ake ciki, sojojin Nijeriya sun ce sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a jihar, tare da ruwaito nasarori a samamen da suka gudanar kwanan nan. TRT Hausa

 
 
 
 
 
#